1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen saman yakin Isra’ila sun kai hari a zirin Gaza.

October 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvNp

Jiragen saman yakin Isra’ila, sun kai hari kan wani yanki na zirin Gaza, don mai da martani ga harba rokokin da Falasdinawa suka yi a kan garin Sedrot da ke kudancin kasar bani Yahudun. Har ila yau dai ba mu sami rahotannin asarar rayukan da aka yi a bangarorin biyu ba. Sai dai, masu sa ido a kan harkokin Gabas Ta Tsakiya sun ce, halin da ake ciki yanzu shi ne mafi muni tun da Isra’ila ta janye dakarunta daga zirin Gaza a watan jiya.

Tashe-tashen hankullan da ake samu yanzu dai na barazanar janyo gocewar yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cim ma tun watanni 8 da suka wuce. Kuma suna dusashe fatar da ake yi na farfado da shawarwarin samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

kungiyar baraden al-Aqsa, wani reshen masu dauke da makamai na kungiyar Al-Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ta ce ita ta kai harin rokoki a kan garin Yahudawa na Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gazan jiya.