1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen yakin Faransa sun kai sabon hari kan IS

Gazali Abdou TasawaNovember 17, 2015

Jiragen yakin Faransa 10 sun kaddamar da sabon hari a birnin Raqa cibiyar Kungiyar IS inda suka lalata wani ofishi da kuma wata cibiyar bayar da horo ga mayakan kungiyar

https://p.dw.com/p/1H6wF
Indien Luftwaffe Kampfflugzeug Mirage 2000
Hoto: Indian Air Force

Jiragen yakin kasar Faransa sun sake kaddamar da wasu sabbin hare-hare a daren jiya washe garin wannan Talata a birnin Raqa cibiyar Kungiyar IS.

Ofishin ministan tsaron kasar ta Faransa wanda ya sanar da wannan labari ya ce jiragen yaki 10 ne sanfarin Mirage 2000 da Rafale da suka taso daga kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Jodan suka kaddamar da harin inda suka jefa bama-bamai 16 kan gurare daban-daban na birnin Raqa inda suka lalata wata cibiyar bayar da umarni da kuma wata cibiyar horas da mayakan kungiyar.