1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiran sakamakon zabe a DRC

August 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bume

A Jamhuriya Demokradiyar Kongo, a na ci gaba da jiran sakamakon zaben yan Majalisun dokoki da na kananan hukumomin da aka gudanar ranar 30 ga watan da ya gabata.

A yau talata hukumar zabe mai zamankanata ta bayana sakamkonwucingadi da ya shafi kashi 40 bisa 100 na yawan muatennda su ka kada kuri´a.

Har yanzu shugaba rikwan kwarya, Joseph kabila ke sahun gaba, tare da kashi kussan 55, bisa 100 na jimmilar kuri´un da a ka jefa.

Mataimakin shugaban kasa, bugu da kari, madugun yan tawaye, Jean Pierre Bemba, na sahu na 2, tare kashi kussan 17 bisa 100.

Wannan sakamako ya kunshi 82, daga cibiyoyin kidayar kuri´u 169 da ke fadin kasar baki daya, sannan ya shafi mutane million 10, daga jimillar million 25 da ya cencenta su kada kuri´u.

Ya zuwa yanzu, hukumar zabe, ta kasa bayana sakamakon Kinshasa, babban birnin kasar, wanda shi kadai, ya share kashi 12 bisa 100, na al´ummomin da su ka jefa kuri´a.

Ranar 20 ga watan da mu ke ciki, ake sa ran samun sakamakon zaben baki daya.