1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin ruwan yahudawa ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza

September 26, 2010

Ƙungiyoyin yahudawa masu kare haƙƙin bil Adama, sun yi lodin jirgin ruwa daga Syprus domin taimakawa al´umar Gaza.

https://p.dw.com/p/PN9o
Jirgin ruwan yahudawa ɗauke da kayan agaji zuwa GazaHoto: DW/AP
Ƙungiyoyin yahudawa 'yan fafutukar kare haƙƙin bil'adama da Isra'ila da Turai da kuma Amirka sun cika kayan agaji ga wani jirgin ruwa domin kaiwa falasɗinawa da ke zirin Gaza, a ƙoƙarin da su ke yi na karya shingen da Isra'ila ta sanyawa masu muradin zuwa yankin. Tuni dai jirgin kayan agajin ya bar ƙasar Cyprus ɗauke 'yan fafutuka takwas ciki har da matuka jirgi ukku da kuma 'yan jarida biyu. Wani bayahuden da ya tsira daga kissan kiyashin Nazi da aka yiwa yahudawa mai suna Reuven Moskovitz - ɗan shekaru 82 da haihuwa, ya ce wani nauyi ne da ya rataya a wuyansa, a matsayin wanda ya tsira daga wancan zaluncin, ya nuna adawarsa ga abinda ya kira kisa, da cin zarafi da kuma sanya al'ummar Gaza cikin fursuna ciki kuwa kamar yadda ya ce har da mata da ƙananan yara da yawan su yakai dubu 800. Shi kuwa Yonatan, wanda kamar Moskovitz ke cikin jirgin, ya ce ba wai suna son yin fito - na - fito ne da Isra'ila ne ba, amma idan sojojin Isra'ila suka dakatar da jirgin, to kuwa ba za su taɓa ƙyalesu kai jirgin zuwa bakin tekun Ashdod ba, inda suka karkatar da akalar sauran jiragen da ke ɗauke kayan agaji ga al'ummar Gaza. Jirgin ruwan dai zai yi tafiya mai nisan sa'oi 36 ne kafin zuwa yankin na Gaza. Ministan kula da harkokin tsaron Isra'ila Ehud Barak ya sha nanata cewar Isra'ila za ta ƙwace duk wani jirgin da ya zo kusa da Gaza, yankin da Ƙungiyar Hamas ce ke da iko da shi. 

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadissou Madobi