1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Kerry yana ziyara a Afghanistan

Suleiman BabayoApril 9, 2016

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gana da manyan jami'an kasar Afghanistan yayin ziyarar ba zata da ya kai.

https://p.dw.com/p/1ISTv
Afghanistan John Kerry und Salahuddin Rabbani in Kabul
Hoto: Reuters/J. Ernst

Sakataren harkokin wajen kasar Amirka John Kerry ya kai ziyarar ba zata zuwa kasar Afghanistan inda ya gana da Shugaba Ashraf Ghani da kuma shugaban hukumomin gwamnati Abdullah Abdullah, wanda yake rike da mukami makamancin firaministan kasar. Kerry yana ziyarar domin karfafa goyon baya ga gwamnatin kasar ta hadaka da Amirka ta taimaka aka kafa tsakanin mutanen biyu wadanda suka fafata zaben shugaban kasa gazaye na biyu.

Kerry zai kuma tattaunawa hanyoyin aiwatar da daukacin yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka, inda wata majiya take cewa za a mayar da mukamun Abdullah Abdullah zuwa firaminista. Yanzu haka akwai kusan sojojin Amirka 10,000 cikin kasar wadanda suke haros da dakarun kasar gami da taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnatin kasar ta Afghanistan tana fuskantar tashe-tahsen hankula daga tsagerun kungiyar Taliban wadanda Amirka ta kawo karshen gwamnatinsu cikin 2001. Akwai kuma matsalolin na tattalin arziki da suka janyo rashin aiki.