1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jos: Musulmi da Kiristoci na siyasa a tare

Gazali Abdou Tasawa
December 22, 2017

A jihar Filaton Najeriya matasan Kirista da Musulmi na cigaba da kafa kungiyoyin siyasa don cudanya da juna gabanin zaben kananan hukumomin da za'a yi cikin jihar a watan Fabarairu na shekara mai zuwa. 

https://p.dw.com/p/2prPJ
Deutschland Hessischer Friedenspreis 2013 an Pastor James Wuye und Imam Mohammed Ashafa
Pastor James Wuye kenan da Imam Nurain Ashafa wanda ke aiki tare don tabbatar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-dabanHoto: picture-alliance/dpa/B. Roessler

Yanzu haka dai akwai ire-iren waddan nan kungiyoyi da dama wadanda suke shiga harkokin siyasa mai makon yadda a baya ake amfani da su wajen yin bangar siyasar. Mr Lemark Peter shi ne babban daraktan kungiyar matasa da ka kira Yes 2019 wadda kungiya ce ta siyasa, ya ce sun hado matasan Musulmi da Kirista ne cikin dandali guda don rika cudanya da juna a siyasance.
 
A shekarun baya dai matasan daga bangarorin biyu sun yi ta kai ruwa rana tsakanin su musamman ma a lokutan zabe, to sai dai yanzu sun ce sun gano 'yan siyasa na amfani da su ne kawai wajen salwantar da rayukan junansu don kawai su sami shugabanci. Dalili kenan da ya sa suka kafa kungiyoyin da za su rika taimakon juna maimakon bangar siyasa. Malam Bala Buswat wani matashi ne daga karamar hukumar kanam ya ce su kan samar wa 'yan uwansu matasa sana'o'i ta hanyar wadannan kungiyoyi da suke kafa wa.
 
Yayin da Najeriya ke tinkarar babban zabe a shekarar 2019, shugabanin matasan na Filato sun hakake cewar za su isar da wannan kyakyawar manufa tasu ga shauran yan'uwansu matasa da ke wasu jihohi musamman ma jihohin da a kan fuskanci tashe-tashen hankula na addini a cewar Mr Polycarp Jurbe mataimakin daraktan kungiyar siyasa ta Yes 2019 a jihar Filato.