1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin mulki a Thailand

Zainab A MohammadSeptember 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bty4
Tankunan Soji a Bangkok
Tankunan Soji a BangkokHoto: AP

Sabon shugaban gwamnatin Mulkin soji na Thailand,yayi alkawarin sauka daga mukaminsa nanda da makonni biyu,tare da gudanar da zaben democradiyya cikin shekara guda,bayan habare gwamnatin prime minista Thaksin Shinawatra,ba tare da zubar da jini ba a jiya.

General Sonthi Boonyaratglin,wanda ya jagoranci juyin mulkin daya gudana a daren jiya talata,yace an hukunta thohon premier Thaksin ne dangane da bukatun alummar kasar,na kasancewa cikin watannin mulki na kunci.

General Sonthi ya sanar da cewa zai yi murabus daga mukamin mukaddashin premien Thailand nanda makonni biyu,domin a halin yanzu suna neman wanda zai hau kujerar Prime minista,kana a watan 0ctoban shekara ta 2007 zasu gudanar da zaben kasa.

Ya kara dacewa wadanda suka cancanci maye gurbin Prime ministan zasu kasance mutane ne yan siyasa wadanda keda raayi na daban,kuma suke da kaunar Democradiyya a zukatarsu,a karkashin Basaraken kasar,a matsayin Shugaban kasa.

Bayan sanar da kifar da gwamnatin kasar dai a daren jiya,Sonthai da sauran genar genar na Thailand din sun gana da sarki BhumibolAdulyadej.

Thailand din dai ta kasance cikin hali na rudani cikin watannin da suka gabata,tun bayan da iyalin premier Thaksin suka sayar da hannayen jari na masanaantar sadarwa,wanda ya kunshi dala billion 2,ba tare da biyan haraji ba.

Sakamakon bore da alummar kasar sukayi ta gudanar akan titunan kasar yasa Mr Thaksin ya sanar da gudanar da zabe a watan Aprilu,tare da sauka daga mukaminsa na wucin gadi,to sai dai zaben ya haifar da wani sabon rikici,wanda ya jagoranci kulle jamian hukumar zaben kasar ,adangane da zargin cewa sun tallafawa jammiyar Mr Thaksin.

Tun bayan nan akayi ta samun jinkiri dangane da gudanar da sabon zabe,wanda akan hakane General Sonthi yace sojoji sukace lokaci yayi da zasu dauki mataki,sai dai ya karyata zargin da akeyi na nacewa da hannun sarki a juyin mulkin.

Hanbararren Premiermn Thailand Thaksin Shinawatra wanda ke halartan taron zauren mdd na 61 a birnin Newyork din Amurka a yayin wannan juyin mulki ,yace baiyi tsammanin sojojin kasar zasuyi masa juyin mulki ba,sai dai yace bazai tilasta kansa kann wannan mukami ba.

Shi kuwa sakatare general na mdd ,kira yayi dangane da bukatar zaman lafiya,domin sama da shekaru 10 kenan da democradiyya ta samu gindin zama a karkashin jagorancin Basaraken Thailand din

Shima jakadan Amuka a mdd John Bolton yayi fatan cewa zaa bi dokokin da suka dace domin warware wannan takaddama.

To sai wannan hali da siyasar Thailand ta tsinci kanta ciki ya haifar da Allah wadan kasashe dake muradin ganin cewa an democradiyya ta samu gindin zama a wannan kasa data fuskanci juyin mulki har sau 18,a shekaru 70 da suka gabata.

Sama da mutane 1,400 suka rasa rayukansu a tashe tashen hankulan shekaru 3 a kudancin Thailand,kuma ana cigaba da fuskantar rikice rikice ,duk da dokar soji da hambararren Premier Thaksin ya kaddamar a wasu yankuna.