1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin mulkin farko a nahiyar Afrika

Sadissou YahouzaOctober 7, 2010

Farkon juyin mulki da sojoji su ka shirya a nahiyar Afrika ya taso daga ƙasashen Masar da Sudan

https://p.dw.com/p/PY7t
Juyin mulki a AfrikaHoto: AP

Ƙasar farko da ta fara shirya juyin mulki a Afrika itace ƙasar Masar a shekara 1952 inda Mohamed Naguib ya kifar da mulkin Sarki Farouk na ɗaya.

Sai kuma a shekara 1958 a ƙasar Sudan mai maƙwabtaka da Masar inda Ibrahim Abdoud ya hamɓarar da shugaba Abdoullah Khalil.

A yankin yammacin Afrika kuwa ƙasar Togo ce ta fara ɗanɗana uƙubar juyin mulki  a shekara 1963 shekaru uku bayan samun ´yancin kai, inda Emmanuel Bodjollé ya kifar da zaɓɓaɓen shugaba na farko Sylvanius Olympio.

Daga ƙasar Togo ne al´adar juyin mulkin ta bazu a sauran ƙasashen Afrika maƙwafta, kamar su Mali, Burkina Faso, Jamhuriya Nijar, Tarayya Najeriya da dai sauran su.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmed Tijani Lawal