1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Köhler a Afurka

April 10, 2006

A ziyararsa ga kasashen Afurka, shugaban kasar Jamus Horst Köhler na samun rakiya daga 'yan kasuwa na kasar

https://p.dw.com/p/Bu0j
Köhler a Afurka
Köhler a AfurkaHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Shugaban kasar Madagaskar Ravalomanana ya yaba wa Jamusawa a game da kakkarfan matsayi da kuma azamar da suke da shi a lokacin ganawarsa da shugaba Horst Köhler. Kasar ta Madagaskar daidai da sauran kasashen Afurka da Köhler ke ziyarta suna madalla da rakiyar da ‚yan kasuwar Jamus ke masa. Dukkan kasashen na Muzambik da Madagaskar da Botswana kasashe ne dake bin manufofi na canje-canje, amma kuma dangantakar ciniki tsakaninsu da Jamus bata taka kara ta karya ba. A saboda haka ‚yan kasuwar daga Jamus ke neman yin amfani da wannan dama domin gane wab idanuwansu halin da ake ciki a game da kasuwannin wadannan kasashe uku, in ji Hans Meier-Ewert, managing-darektan kungiyar ‚yan kasuwar Jamus dake da jari a Afurka. Meier-Eawert ya kara da cewar:

Manufar tawagar ‚yan kasuwar ita ce domin su nakalci yanayin da wadannan kasashe ke ciki. Kuma a hakika mun lura da irin kyakkyawan ci gaban da ake samu a kasar Muzambik, ko da yake al’amura a kasar sun banbanta da yadda suke a Jamus. Wajibi ne mutum ya raba hannu a maimakon zuba jari a wani bangare guda daya kwal. Wannan na nuni ne da mawuyacin halin dake akwai, amma kuma wata kyakkyawar dama ce ta samun riba iya gwargwado.

Ita dai Muzambik tana daya daga cikin kasashe goman da suka fi fama da talauci a duniya kuma tana tinkaho ne da kamfaninta na sarrafa karafa dake da jarin Afurka ta Kudu. Kasar tafi dogara ne akan ayyukan noma da kamun kifi. Dangane da Madagaskar kuwa shugabanta Ravalomanana na daukar tsauraran matakai na garambawul ga tattalin arzikin kasar, wadda ta sha fama da tsare-tsaren gurguzu da manufofi na dogon Turanci. Gwamnati na fatan yin gyara ga hanyoyinta na sadarwa da gina sabbin hanyoyin mota da nagartattun kafofin samar da ruwa da wutar lantarki domin bunkasa ayyukan yawon bude ido da kasar ta dogara akai domin samun kudaden shiga. Ita kuwa Botsawana, in aka ajiye maganar cutar kanjamau dake addabarta, kasa ce dake samun bunkasar tattalin arziki a cikin gaggawa fiye ma da sauran sassa na duniya kuma ba ta bukatar taimako na raya kasa. To sai dai kuma wannan bunkasar ta dogara ne akan cinikin damenti da Allah Ya albarkaci kasar da shi, wanda kuma ke samar mata da kashi 80% na kudaden musaya na ketare. Babban aikin da gwamnati ta sa gaba a yanzun shi ne neman wasu sabbin hanyoyin da zasu taimaka wa tattalin arzikinta a dangantakunta na ciniki da kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka da kuma kasashen kudancin Afurka dake makobtaka da ita.