1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140510 China D

May 16, 2010

Shugaban tarayyar Jamus zai gana da takwaransa na ƙasar China a Beijing, kana zai ziyarci Shanghai inda ake bikin baje koli wato Expo

https://p.dw.com/p/NPH9
Horst KoehlerHoto: picture alliance/dpa

Shugaban Tarayyar Jamus Host Köhler yana ziyar dake cike da tarihi a ƙasar China, a ci gaban dangantakar ƙasashen biyu. A lokacinda shugaban gwamnatin Jamus na farko ya ziyarci ƙasar China a shekara ta 1975, ya kwatanta ƙasar China a matsayin wata duniya daban mai ban sha'awa.

A dai dai lokacin ƙasar China take ƙara bunƙasa haka ma dangantakar ta ƙasar Jamus ke ƙaruwa. Kamfanin ƙira motoci na Volkwagen, shine kamfanin mota na farko da ya fara zuwa ƙasar China, inda kuma ya buɗe babban rashensa a ƙasar. Tun daga lokacin dangantaka ta ci gaba da wanzuwa tsakanin ƙasashen har izuwa shekara ta 1989, lokacin da China ta murƙushe masu zanga zangar neman a kafa mulkin dimokraɗiya. Shugaban gwamnatin Jamus na wancan lokacin Helmurt Kohl ya nuna ɓacin ransha, abinda kuma ya raunata dangantaƙar ƙasashen biyu.

"Muna makoki tare da Sinawa, dama sauran ƙasashen duniya, kuma mu da abokanen mu, muna Allah wadai da wannan rashin imanin da ya faru a China"

Amma daga bisa ni Helmut Kohl da kansa, ya sake ɗinke ɓarakar su da China, inda ya ƙarfafa hulɗar tattalin arziki a tsakaninsu, haka kuwa shima Gerhard Schröder wanda ya biyo bayan Kohl. To Amma sai a lokacin shugabar gwamnati Jamus ta yanzu Angela Merkel, aka fara taɓo batun kare haƙƙin bil'adama, inda har ta kai Jamus ta karɓi jagoran 'yan Tbiet Dalai Lama, abinda ya ɓatawa Beijing rai. To amma dai Jamusawan sun fara lallamin Sinawa, domin bayan aukuwar lamarin China ta soke ganawar ministocin ƙasashen biyu, kuma ta soke ƙwangilolin ƙasashen Turai masu yawa. To sai dai Merkel ta kare matakin da ta ɗauka.

"Ina ganin dangantakar Jamus da China tafi ƙarfin batun Dalai Lama, kyawawan tsarin da muka yi, da waɗanda suka gabacemu suka yi, ba abune da za'a iya kwatantawa ba"

Shekara guda bayan fishin da Jamus ta tsokalo, a dai dai lokacin da ake fama da matsalar tattalin arzikin duniya, Firimiyan ƙasar China Wen Jiabao ya ziyarci Jamus, don tattauna matakan da ƙasashen biyu za su ɗauka.

"Mu Sinawa muna da wata karin magana, inda muke cewa, idan ka ga anyi ƙanƙara mai yawa, to shekarar za'a samu kykkyawar damina. Don haka ina da tabbaci a wannan hunturu za mu samu bakin zaren matsalar"

Banbance-banbancen tsakanin ƙasashen biyu dai suna da yawa. Baya ga batun kare haƙƙin bil'adama, Jamus tana son taimakon China wajen matsawa Iran da Koriya ta Arewa a taƙaddamar nukiliyarsu da ƙasashen yamma. Ita kuwa China ba ta baiwa ƙasashen yamma jiki, domin tana ganin suna adawa da irin bunƙasar tattalin arziki da take samu.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Mathias Bölinger

Edita: Mohammed Nasiru Awal