1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Köhler Muzambik

April 5, 2006

A rana ta biyu ga ziyararsa ga Muzambik shugaban kasa Horst Köhler ya mayar da hankalinsa ga dangantakar al'adu

https://p.dw.com/p/Bu0q
Köhler da Mandela
Köhler da MandelaHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

A baya ga jami’an siyasar kasar ta Muzambik, shugaban kasar Jamus Horst Köhler, kazalika ya sadu da tsofon shugaban kasar Afurka ta Kudu Nelson Mandela wanda ya ce wani gwarzo ne na tarihi. A rana ta biyu ga ziyarar tasa shugaban na Jamus zai mayar da hankalinsa ne ga manufofi na tattalin arziki da al’adu. Bisa ga ra’ayin Köhler dai kasashen Turai ba sa ba da la’akari sosai yadda ya kamata ga al’adu da kuma tarihin nahiyar Afurka, inda ya kara da cewar:

“Wani muhimmin abu a gare ni shi ne ganin cewar kasashen Turai, abin da ya hada har da Jamus sun nemi karin ilimi a game da nahiyar Afurka. Gidan wasan kwaikwayon Avenida shi ne daya kwal dake akwai a duk fadin kasar Muzambik. Amma a daura da haka al’amura kasar na amfani da fasahar wasannin kwaikwayo da zane domin bayyana irin mawuyacin halin da suke ciki. Wannan na mai nuna mana irin zurfin tunani da kaifin hankalin dake tattare da al’umar Afurka ne. Muddin muna fatan fahimtar yanayi daban-daban na wannan duniya tamu da kuma irin albarkatun da ta kunsa to kuwa wajibi ne mu gane cewar a wannan bangaren Allah Ya yi wa nahiyar Afurka wadata mai yawa.”

Shugaban kasa Horst Kähler ya kara da jaddada cewar dangantaka da ba da hadin kai ga kasashen Afurka ba ya dogara akan taimakon kudi ne kawai ba. Muhimmin abin dake akwai shi ne ba da cikakken goyan baya ga wasu shirye-shiryen rayawa wadanda zasu taimaka wajen daga matsayin nahiyar Afurka da kuma amfani da wadatar fasaha da Allah Yayi wa al’umarta ta yadda za a rika damawa da wannan nahiya kafada-da-kafada a siyasar duniya. Shugaban yayi alkawarin gabatar da wani shiri na sukalaship ga masana na Afurka domin daga matsayin ayyukan binciken kimiyya da fasaha a wannan nahiya. Ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus ita ce zata dauki nauyin wannan shiri.

Dangane da kasar Muzambik kuwa Köhler ya ce har yau da sauran rina a kaba wajen magance matsalar cin hanci da tabbatar da aikin doka da tsarin mulki na demokradiyya. Wannan maganar ta kara fitowa fili a tattaunawar da shugaban yayi da ‘yan kasuwar Jamus dake da jari a kasar ta kudancin Afurka. Amma duk da haka Köhler ya ce kasar tana kan wata kyakkyawar hanya madaidaiciyar da zata kai ta ga tudun na-tsira, musamman ma ta la’akari da zaman lafiya da kwanciyar hankalin da take da shi bayan shekaru gwammai na yakin basasa. In kuma ta ci gaba akan haka kasar ta Muzambik zata wayi gari tana mai daukar hankalin ‘yan kasuwa na ketare domin zuba jari a cikinta, lamarin da zai ba ta damar yakar matsaloli na talauci da karancin ilimi tare da samar da guraben aiki ga matasanta.