1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Köhler a Afirka

Schaeffer, Ute (DW-Afrika/Nahost)February 6, 2008

Ziyarar shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler zuwa Afirka.

https://p.dw.com/p/D1hJ
Shugaba Köhler da wasu shugabannin AfirkaHoto: AP

►Rikicin ƙasar Kenya ya nunar a fili yadda wata gaba ta ƙabilanci ke iya rikiɗewa zuwa wani rikicin siyasa. A saboda haka batun Kenya zai kasance muhimmin batun da shugaban Jamus Horst Köhler zai fi mayar da hankali kai a tattaunawar da zai yi a ƙasar Uganda. A yau lahadin nan shugaban na Jamus yake fara rangadi karo na biyar a Afirka inda zai kai ziyara a Uganda da kuma Rwanda, ƙasashen da suka yi fama da tashe tashen hankula da yaƙe-yaƙe. Mohammad Nasiru Auwal na ɗauke da ƙarin bayani.◄


A ƙarkashin taken hanyoyin samar da zaman lafiya da sasantawa a Afirka shugaban tarayyar Jamus Horst Kähler ya fara rangadinsa karo na biyar a gabashin nahiyar Afirka. Zaman lafiya na zaman ginshiƙin samun ci-gaba. Tun ba yau ba yaƙe-yaƙe da rikice rikice suke kawo babban cikas ga ci-gaban ƙasashen wannan yankin.


A saboda haka Köhler ya fara wannan rangadi a Uganda da Rwanda ƙasashen da ke da kyawawan dangantaku da Jamus sannan a fannin haɗin kan aikin raya ƙasa musamman a ɓangeren wanzar da zaman lafiya Jamus ke taka muhimmiyar rawa a cikinsu. Dukkan ƙasashen biyu dai suna ƙoƙarin yin sulhu mai wahala. Uganda a dangane da yaƙin basasa sannan Rwanda dangane da kisan kiyashin shekara ta 1994.


Banbanci tsakanin ƙasashen biyu na da yawa saboda haka shugaban na Jamus zai nemi cikakken bayani game da taimako mafi dacewa daga ƙetare da kowace daga cikin ƙasashen biyu take buƙata.


Köhler:

Köhler ya ce "A Turai da ma Jamus ba mu da cikakkiyar masaniya dangane da bambamci dake akwai a Afirka. Ba za mu iya yanke hukunci da cewa dukkan ƙasashen Afirka matsalolinsu iri guda ne ba. Saboda haka ya zama wajibi mu bambamta manufofinmu ta yadda za su dace da bukatun kowace ƙasa a wannan nahiya."


Uganda ta daɗe tana zaman wata ƙawar Jamus a aikin raya ƙasa. Amma yaƙin basasan da aka shafe shekaru 20 ana yi arewacin ƙasar ya sa an dakatar da wannan aiki. Rikicin tsakanin sojojin ƙungiyar ´yan tawayen Lord´s Resistance Army da dakarun gwamnati ya janyo asarar rayuka fiye da yaƙin Iraqi. Yanzu haka dai gwamnati a Kampala ta gane cewa sai tare da kyakkyawar manufar aikin raya ƙasa a arewacin Uganda, mutane kimanin miliyan biyu da aka tilastawa barin yankin za su iya komawa gida. Henry Oryem Okello sakataren ƙasa a ma´aikatar harkokin waje ya yi nuna da cewa an ɗauki lokacin mai tsawo ana mayar da yankin saniyar ware.


Okello:

Okello ya ce "Abin da muka sa a gaba yanzu shi ne aiwatar da aikin raya arewacin Uganda wanda ya yaƙin basasan shekaru 20 suka yiwa kaca-kaca. Za mu tafiyar da aikin sake gina wannan yanki saboda haka muna neman taimako a wannan ɓangare."


A cikin shekaru 20 da suka wuce Jamus ta bawa Uganda Euro miliyan 500 a matsayin taimakon raya ƙasa sannan a watan Afrilun bara an yi mata alƙawarin ba ta euro miliyan 56 daga wannan shekara zuwa ta 2010 wato ƙarin kashi 25 cikin 100.


A cikin shekarun bayan nan dai Uganda ta samu nasarar rage yawan talauci da masu ɗauke da kwayoyin cutar HIV ya zuwa ƙasa da kashi 7 cikin 100. Sanna yawan yara da ke shiga makaranta ya ƙaru zuwa kashi 90 cikin 100. To sai dai ƙasar na fama da matsalar cin hanci da rashawa ƙarƙashin shugaba Yoweri Museveni wanda ke tursasawa ´yan adawa da kuma ´yan jarida.


Ita ma Rwanda tana samun ci-gaba a fannin ba da ilimi. Shugaba Kagame na aiwatar da sauye sauye na siyasa kamar yadda ƙungiyar tarayyar Afirka ta nema. Tana ɗaya daga cikin ƙasashen na farko da suka cike ƙa´idojin NEPAD. A tattaunawar da zai yi a birnin Kigali shugaba Köhler zai taɓo wannan ci-gaba da Rwanda ta samu da kuma ƙokarin da take yi na yin sulhu tsakanin al´ummomin ƙasar.