1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kace nace game da jawabin Chirac a Jamus

January 23, 2006
https://p.dw.com/p/BvB0

Jam´iyyun adawa na tarayyar Jamus, sun bukaci shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel data yi nesa da shirin shugaba Jacque Chirac na amfani da makaman nukiliya.

Wannan kira daga bangaren jam´iyyun adawar yazo ne a dai dai lokacin da shugabar ta Jamus zata fara ziyarar aiki izuwa kasar ta Faransa a yau din nan.

Jam´iyyun na The Greens da kuma ta masu neman canji, sun bukaci , shugaba Angela Merkel data yi amfani da wannan damar wajen nunawa kasar ta Faransa cewa Jamus na adawa da kalaman da shugaban kasar ta Faransa yayi a makon daya gabata.

To sai dai kuma daya daga cikin jami´an jamiyyar CDU mai mulkin kasar, wato Eckart Von Klaeden, cewa yayi bai ga dalilin sukar matakan gwamnatin na Faransa akan yin amfani da makamin nukiliyar ba.

Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Jacque Chirac na Faransa yayi barazanar yin amfani da makaman nukiliya wajen yaki da ayyukan yan ta´adda, ko kuma kai hari ga duk wata kungiyya ta yan ta´adda data kawo mata hari.