1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kace-nace kan kasafin kudi a Najeriya

Uwais Abubakar Idris/LMJMay 4, 2016

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake mayar da kasafin kudin kasar ga majalisar dokoki sakamakon rashin amincewa da gyare-gyaren da suka yi a ciki.

https://p.dw.com/p/1IiSM
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Wannan takaddama ko kuma kiki-kaka dai na haifar da kace-nace, inda kwararru ke tsoron ka iya shafar aiwatar da kasafin kudin kansa. Kiki-kakar da ke faruwa a game da kasafin kudin Najeriya na 2016 dai, ta kara daukan sabon salo ne biyo bayan kara bude idanun da bangaren zartaswan ke yi a kan wannan lamari, wanda shi ne irinsa na farko da ake gani a demokradiyyar Najeriyar.

Wankin hula na shirin kaiwa dare

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Ginin majalisar dokokin Najeriya da ke AbujaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Abin dai ya fara kamar wasa, sai dai a yanzu na neman zama wanki hula zai kai sassan biyu dare, domin kuwa a karo na uku a jere kenan Shugaba Buhari na mayar da kasafin kudin ga majalisar bisa zargin aringizo da kara wasu kudi na radin kai da ‘yan majalisar suka yi. Ahmed Babba Kaita dan majalisar wakilai ne kuma ya tabbatar da cewa an sake mayar da kasafin kudin. To sai dai tuni kwararru irin su Mallam Yusha'u Aliyu kwararre a fannin tattalin arziki, suka fara koke kan irin illar da wannan jinkiri ka iya yi ga aiwatar da kasafin kudin kamar yadda ya kamata.

Talakawa na ji a jiki

Mafi yawan 'yan Najeriya dai na jiran sanya hannu kan kasafin kudin sakamakon fatan da suke da shi na ko zai iya sauya yanayi da ma halin ukuba da suka shiga a kasar, duk da cewa mafi yawansu na goyon bayan Shugaban. ‘Yan majalisar dai na cewa akwai bukatar a yi aiki da fahimta a kan wannan lamari.

Nigeria Abuja Proteste Regierung
'Yan kungiyar "Occupy National Assembly" lokacin zanga-zanga a gaban majalisar dokokiHoto: DW/U. Musa

A yayin da wasu ke tsoron illar da jinkirin ka iya haifarwa a hangen dan majalisa Ahmed Babba Kaita, na hangen alhairi ga 'yan Najeriya daga wannan jinkiri da ma ji a jikin da suke yi. Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, kwamitocin kula da kasafin kudi na majalisun dattawa da wakilai na can suna taro a kan gyare-gyaren da shugaban Najeriyar ya dage dole sai an aiwatar kafin ya sanya hannu a kasafin kudin da ‘yan Najeriya ke dako a wani fata na samun sauyi.