1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kace-nace tsakanin kasashen Turai da Amirka game da kwangilar sake gina Iraqi.

Mohammad Nasiru AwalDecember 11, 2003
https://p.dw.com/p/BvnB
Ko shakka babu Paul Wolfowitz ya yi riga malam masallaci, inda ya ba da sanarwar cewa duk kasar da ba ta shiga cikin yakin da Amirka ta yi da Iraqi ba, ka da ta sa rai na samun kwangilar da za´a raba don sake gina Iraqi. Wadannan kalaman dai rashin basira, musamman a wannan lokaci da ba a dade da dinke barakar da ta taso tsakanin gwamnatocin biranen Washington, Berlin, Paris da Mosko ba. Jim kadan bayan furucin, shugaba GWB ya yi saurin tuntubar gwamnatocin biranen Berlin, Paris da Mosko don kauracewa aukuwar mummunan rashin jituwa. Ko shakka babu kalaman na mista Wolfowitz ba su sha bambam da wadanda watakila su kansu kasashen Turan da abin ya shafa, zasu furta ba. Su ma kasashen Turan wadanda yanzu suke tayar da jijiyar wuya tare da yin barazanar kai wannan batu gaban kungiyar ciniki ta duniya, su kan ba da taimakon raya kasa ne idan kasar da zata karbi wannan taimako ta tabbatar da cewa zata saye kayakin wadannan kasashe. Bugu da kari kuma kasashen yankin da Amirka ta kira tsohuwar Turai, sun fusata, lokacin da gwamnatin Poland, sabuwar kasar da za´a dauke ta cikin kungiyar EU, ta yi amfani da kudaden taimako da kungiyar ta ba ta wajen sayen jiragen sama daga Amirka. Ayar tambaya a nan itace, me yasa a game da batun na Iraqi ya kamata gwamnatin Washington ta yi wani abu dabam? Dole ne a dubin hakan da idanun basira, domin da kudin talakawan Amirka ne za´a yi aikin sake gina Iraqin, kuma dole shugaba Bush yayi taka tsantsan a wannan lokaci da ake shirin fara yakin neman zaben shugaban kasa.

Shi yasa amfani da dokokin kasashen duniya a wannan halin yana da babban hadari, domin babu wata shaidar dake nuni da cewa kasashen Turan zasu samu nasara. Domin ka´i´dojin yarjejeniyoyin Haag da Geneva game da yankunan da aka mamaye, sun dorawa kasar da ta mamaye wani yanki alhakin sake gina wannan yanki da ta mamaye, don saukaka halin rayuwar al´umar wannan yanki.

Ko da yake kasashen Turan sun jawo hankalin Amirka game da wadannan ka´idojin, amma ba su nuna wani shirin ba da taimakon sake gina Iraqi ba. Alal misali a gun taron birnin Madrid na kasashen da zasu ba da taimakon sake gina Iraqi, kasashen Jamus da Faransa da kuma Rasha sun yi dari-dari wajen bayyana irin gudumawar da zasu bayar bisa manufa. Yayin da Amirka kuwa ta kuduri aniyar ba da kashi 2 cikin 3 na zunzurutun kudi dala miliyan dubu 30 da ake bukata. Me yasa yanzu kasashen Turan ke son a yi kashe muraba a kwagilar da Amirka zata bayar wajen sake gina Iraqi?

Wasu cewa ma suka yi mayar da kamfanonin Turai saniyar ware a wannan harka, zata yi babbar illa ga al´umar Iraqi, sai ka ce kamfanonin Jamus da na Faransa da kuma na Rasha sun yi takwarorinsu na Amirka kwarewa. A taron birnin Madrid, wakilan gwamnatin Iraqi sun bayyana cewa har abada al´umar Iraqi zasu tuna da wadanda suka taimaka musu lokacin da suke cikin kunci da wadanda suka juya musu baya.