1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KADDAMAR DA YAKIN NEMAN ZABEN SHUGABAN KASA A AFGANISTAN.

September 7, 2004

Yau ne aka kaddamar da Kampaign na yakin neman zabe a Afganistan.

https://p.dw.com/p/Bvgg
Shugaba Hamid Karzai na Afganistan,kuma Dan takara.
Shugaba Hamid Karzai na Afganistan,kuma Dan takara.Hoto: AP

An kaddamar da shirin Campaipn na zaben shugaban kasa karon farko a afganistan,zaben dake zama zakaran gwajin dafi a yunkurin da Amurka keyi na sake gina wannan kasa ,bayan yakin daya hambarar da gwamnatin yan taliban masu tsattsaurar raayi.

Rahotanni daga Afganistan din dai nuni dacewa mayakan Taliban sun lashi takobin kawo cikas cikin harkokin zaben shugaban kasa da Amurka ta dauki nauyin gudanarwa ranar 9 ga watan Oktoba mai tsayawa,zaben da shugaba Bush na Amurkan ke fatan gudana ba tare da wata matsala.

Abdul Latif Hakimi na kungiyar yan Taliban,a hiran da yayi da wakilin Reuters ta wayar Tangaraho,yace idan har basu saurari gargadin da sukayi musu ba,zasu kuka da hawayensu.Duk dacewa baa bayyanar da kaddamar da wannan Campaign na yau ba,akasarin mazauna birnin Kabul na sane dacewa ,shirin Campaign din na nan tafe.

Wadanda akayi hira dasu sunyi fatan cewa zaben zai gudana cikin lumana.

A shekara 2001,shugaba Bush na Amurka ya afkawa Afganistan da karfin Soji,da nufin hambare gwamnatin Taliban masu tsattsauran raayi,bayan gwamnatin tayi watsi da batun mika shugaban kungiyar Al Qaeda Osama bin Laden.

Ana dai ganin cewa Shugaban gwamnatin Rikon kwarya na yanzu Hamid Karzai,wanda keda goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammaci,zai samu nasara a wannan zabe,koda yake yana da abokan takara masu karfin gaske.

Shugaba Bush na kokarin kafa zababbiyar gwamnati a Afganistan,a matsayin nasara ta fannin manufofinsa na kasashen ketare,wanda kuma zai iya gyara masa kalubale dayake fuskanta da suka kann harin daya afkawa Iraki dashi babu gaira ba dalili.

Kasar ta Afganistan dai na fuskantar matsaloli na rashin tsaro,inda ya zuwa yanzu akwai tabbacin cewa sama da mutane 1,000,da suka hadar da Sojoji,yan yakin Sunkuru,jamian zabe,da masu ayyukan agaji da fararen hula sun rasa rayukansu cikin watanni 12 da suka gabata.

Banda barazanar yan yakin sari ka noke,gazawan gwamnati wajen kwance damaran yakin mayakan shugabannin hauloli ,na cigaba dayin barazana wa harkokin zaben musamman a garuruwa dake arewaci da yammacin Afganistan.

Yan Taliban din dai sunyi alkawarin afkawa dukkan yan takara 18 na kujeran shugaban kasa,da yan takaran majalisar dazai gudana badi,da kuma dukkan wadanda zasu fito domin kada kuriunsu.Adangane da hakane Abdul Latif Hakim,yake shawartan yan takaran da sauran jamaa dasu guji shiga harkokin zaben wannan kasa,idan har suna muradin rayukansu.

A yayin wannan campaingn na yakin neman zabe,wanda zai gudana daga yau zuwa 6 ga watan gobe,anyi alkawarin bawa kowane dan takara yancin amfani da kafofin yada labaru na gwamnati,tare da gudanar da Rally da gabatar da jawabai na kampaign a dukkan gunduwowin kasar.A Birnin Kabul da Kewaye,ana iya ganin Hotuna babban mai kalubalantar Karzai Yunus Qanuni,tare da sauran kananan abokan takararsa.Rahotanni sunyi nuni dacewa hotunan Karzai kalilan ne ke manne acikin fadar kasar dama kewayen Afganistan.Mutane million 10 da rabi ne sukayi regista domin kada kuriunsu,daga cikin kimanin million 25 zuwa 28 na adadin jamaar Afganistan din.

Zainab Mohammed.