1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kaddamar da zaben yan majalisar dokoki a Iraqi

December 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvGr

A yau ake kaddamar da karon farko na zaben yan majalisar dokokin Iraqi,a inda masu jefa kuria a asibitoci,sansanonin soji da gidajen yari na kasar zasu jefa kuriarsu a zaben da kasar Amurka take fatar zai kawo karshen hare hare a kasar domin baiwa dakarunta damar komawa gida.

Gwamnatin kasar Iraqin ta sanarda cewa daga gobe talata idan Allah ya kaimu, zata rufe dukkan bakin iyakokinta,tare da kara lokacin dokar hana fitar dare da hana tafiye tafiye,don kare abinda ta kira kutsowar sojojin sa kai.

Masu jefa kuria a Iraqin zasu kada kuriarsu karo na farko na majalisar dokoki bisa tsarin mulkin kasar tun 2003.

Sabuwar majalisar dokokin da zaa zaba ita keda alhakin zaben sabuwar gwamnati da Amurka take ganin zata samu karbuwa wajen yan sunni.

Cikin wata sanarwa kuma da hukumar zabe ta Iraqin ta bayar tace tana binciken yawan sunayen masu kada kuria na Kirkuk da ya nunka ribi 5 yawan wadanda akayiwa rajista tunda farko.

Kurdawa dai suna kokarin ganin wannan yanki mai yawan arzikin man fetur ya fada cikin yankin cin gashin kansu.