1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa sabuwar Gwamnati a Iraki

Hauwa Abubakar AjejeMay 9, 2006

Sabon Firaminista na Iraq,Nuri al-Maliki ,yace yana fatar kafa cikakkiyar gwamnati a Iraqi cikin kwanaki 2 .

https://p.dw.com/p/Bu0G
Hoto: AP

Firaminista al-Maliki wajen wani taron manema labarai a yau,yace yana fatar kafa gwamnatin ce yau ko gobe,mataki da Amurka take ganin shine kadai zai kare kasar fadawa cikin yakin basasa.

Al-maliki yace abubuwa kadan ne suka saura yanzu,saboda a cewarsa an samu ci gaba mai maana,inda yace sun kamala kashi 90 cikin dari,na ababen da suka kamata.

Wannan nasara da aka samu kuwa,sakamakon matsin lamba daga Amurka,yazo ne bayan kungiyoyin adawa na sunni da qurdawa da kuma shia sun amince da bada mukaman ministocin tsaro dana harkokin cikin gida ga wadanda basu da alaka da kungiyoyi masu dauke da makamai.

Wannan ya nuna cewa,dole ne ministan harkokin cikin gida maici yanzu,Bayan Jabur dole ya sauka daga wannan mukami,tunda shi memba ne na bangaren jamiyar shia dake da kungiyar masu dauke da makamai ta Badr,kuma an zarge shi da alaka da wannan kungiya,kodayake ya karyata zargin.

Jakadan Amurka a Iraqin ya baiyana a fili cewa,Amurka bata kaunar kasancewar Bayan akan wannan mukami.

Karkashin dokar tsarin mulkin kasar,Maliki yana da waadin zuwa ranar 22 ga watan mayu da muke ciki daya mika sunayen ministocinsa ga majalisa,wadda zata yi zamanta a ranar laraba.

Kodayake har yanzu akwai gurabun maaikatun kula da albarkatun mai,cinki da zirga zirga da baa cike su ba,kodayake al-Maliki yace zaa magance wannan batu a yau din nan.

Maliki wanda ake ganinsa a matsayin wani mai tsatsauran raayi na shia,yace zai mika tayin hadin kai ga yan tawayen sunni da suka ajiye makamansu,suka kuma rungumi shirin siyasa da Amurka take goyawa baya.

Kasar Amurkan tana fata kafa wannan sabuwar gwamnati a Iraqi,zai taimaka a kawo karshen kwararar sojojin sa kai larabawa zuwa kasar ta Iraqi,ya kuma baiwa Amurkan damar fara janye sojojinta 133,000 daga kasar.Amurkan dai a ahalin yanzu tayi hasarar sojojinta 2,420.

Cikin tashe tashen hankula na yau a Iraqin,yan sanda sunce sun tsamo gawarwakin wasu mutane 11 cikin kogin Tigrism9 daga cikinsu an yanke musu kawuna,ciki har da yaro dan shekara 10.

Yan sandan sunce dukkaninsu an daure hannayensu,kuma an kashe sune kwanaki 5 da suka shige.7 daga cikinsu suna sanye da kayan jamian tsaro na Iraqi.

A kirkuk,wasu yan bindiga sun harbe sojin Iraqi daya,2 suka raunata,akan hanyar zuwa Tikrit.

A can Ramadi kuma an kashe yan sanda 4 yayinda suke fitowa daga hedkwatarsu a cikin garin na Ramadi

Babu dai wanda ya san dalilin kashe wadannan mutane,sai dai kuma zubda jinni na dariku ya tilastawa dubban jamaa sun tserewa gidajensu