1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa sabuwar gwamnatin Iraki

November 11, 2010

Nuri-Al-Maliki zai ci-gaba da rike masayin Framinista a sabuwar gwmnatin gamin gambiza

https://p.dw.com/p/Q6EB
Firaministan Iraqi Nuri al-Maliki.Hoto: AP

Bayan watannin takwas ana fama da takaddamar siyasa a kasar Iraki, yan majalisar dokokin kasar sun sa hannu akan wata yarjejeniya ta kafa gwamnatin gamin gambiza. A karkashin yarjejeniyar Nuri Al- Maliki zai cigaba da rike mulkinsa na Firaminista har tsawon shekaru fudu masu zuwa

Bangarorin masu rikici akan mulkin sun cimma wannan yarjejeniyar ce bayan da kawance jam'iyyun Irakiyyar da mabiya darikar Sunni ke goyon baya suka amince su shiga a dama da su a cikin sabuwar gwamnatin a karkashin fraministan.

Mawallafi: Abdurahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu