1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafando: Zabe, nasara ce ga Burkina Faso

Gazali Abdou TasawaNovember 29, 2015

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso Michel Kafando ya danganta nasarar gudanar da zabe da wani ci gaba a kokarin dora kasar kan tafarkin demokaradiyya.

https://p.dw.com/p/1HEQ9
Burkina Faso Wahl in Ouagadougou Präsdentschaftskandidat Michel Kafando
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Renaut

A lokacin da ya yi wajabi bayan da ya kada kuri'arsa Michel Kafando ya ce gwamnatinsa ta cika alkawarinta na gudanar da zabe shekara guda bayan fara rikon kwarya. Tun a ranar 11 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai aka so shirya wannan zabe, amma aka dageshi bayan komabayan da aka samu a sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 17 ga watan Satumba kafin su sake mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya a bisa matsin lambar kasashen duniya.

Mutane kimanin miliyan biyar da rabi ne daga cikin kusan miliyan 20 da kasar ta kunsa suka cancanci kada kuri'ar a wannan zabe mai cike da tarihi da ya kasance na farko da kasar ta shirya domin zaben wani shugaba farar hula a karkashin tsarin demokaradiyya:

Wata mace da ta kada kuri'a ta ce "mu abin da muke jira daga sabon shugaban shi ne ya maida hankali kan matsalar mata da ta ilimi da kuma aiki."

'Yan takara 14 ne suka fafata a zaben shugabancin kasar a wa'adin mulki na shekaru biyar.