1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafofin yada labarai a kasashen Larabawa

September 9, 2004

Ga alamu an shiga wani sabon yayi na mahawara a kasashen Larabawa da na Musulmin duniya a game da tashe-tashen hankula da ta'addancin dake dada zama ruwan dare tun bayan tabargazar nan ta garkuwa da 'yan makaranta da aka yi, inda a karshe daruruwan mutane suka yi asarar rayukansu a can kasar Rasha makon da ya wuce.

https://p.dw.com/p/Bvgc

A cikin wani sharhin da ya gabatar a karshen makon da ya gabata dangane da tabargazar garkuwa da kanan yara ‘yan makaranta a kasar Rasha, babban editan tashar nan ta Al-Arabiyya dake Dubai, Abdurrahaman Rashid yayi suka da kakkausan harshe akan abin da ya kira matsalar ta’addancin dake neman zama kayar kifi a wuyan Musulmi. Ba tare da wata rufa-rufa ba jami’in ya fito fili yana mai kokawa a game da yake gani wata al’ada ta yada farfagandar tashe-tashen hankula a kafofin yada labaran kasashen Larabawa a kokarin susa wa mutane wurin dake yi musu kaikai. Wannan wata mummunan tabo ne dake nema ya zama ruwan dare a tsakanin matasa a kasashen Larabawa kuma wajibi ne a warkar da shi tun kafin ya zama gagara-badau. An kuwa jima da yawa daga masu sha’awar kawo canji ga manufofin kasashen Larabawa na dauke da irin wannan ra’ayi, amma ba wanda ya kasa kunne ya sauraresu, a maimakon haka ma kafofin yada labarai na gwamnati kan sa kafa su yi fatali da su. Shi kuwa Abdurrahaman Rashid ya zama tilas a ji ta bakinsa, saboda kasar Saudiyya ce ke daukar nauyin tasharsa ta al-Arabiyya da kuma mujallar Sharkul-awasad da gabatar da sharhinsa. A karshen mako an saurara daga Sarki Fahad na Saudiyyar dake fama da rashin koshin lafiya yana mai yin kira ga malamai da su rika koya wa yara madaidaiciyar hanya ta so da hakuri da juna da addinin Musulunci ya tanada. Shi ma ministan ilimi na kasar Mohammed Rasheed, a karshen mako, ya fito fili yayi gargadin cewar za a kori malamai masu yada akidar gani kashe-ni ko zazzafan ra’ayi na kishin addini daga bakin ayyukansu. Ga alamu kasar ta Saudiyya tana mayar da martani ne akan matsin lambar da take fuskanta a cikin gida da ketare. A can cikin gida ‘yan ta’adda na barazanar tayar da zaune tsaye, sannan daga ketare kuma fadar mulki ta Riyadh na fama da matsin lamba a game da daukar matakan yaki da ta’addanci ba sani ba sabo, tun bayan hare-haren nan na sha daya ga watan satumban shekara ta 2001. A dai wannan marra da ake ciki akwai tababa a game da ko Ya-Allah wannan korafi da Abdurrahaman Rashid yayi zai yi wani tasiri akan manufa. Domin kuwa su kansu ‘yan kama-karya na kasashen Larabawa su kan yi watsi da ainifin matsalolinsu na cikin gida suna masu kokarin kakkabe kansu daga alhakin mawuyacin halin da jama’a ke ciki a kasashensu.