1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalar ruwan tekun Maliya

Abba BashirJanuary 2, 2006

Shin kalar ruwan tekun Maliya ja ne

https://p.dw.com/p/BvVe
Tekun Maliya
Tekun MaliyaHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon, ta fito daga hannun Malam Bagudu Chindo, mazauni a jihar Agadas da ke Jamhuriyar Nijar.Malamin ya ce don Allah ina so ku yi min cikakken bayani, wai shin ita Bahar-maliya da Turawa su ke kiranta da suna “Red sea’’ wato jar teku. To wai ruwan tekun ja ne, ko kuwa yaya abin yake ne?

Amsa: Ita dai tekun Bahar-Maliya wadda Larabawa suke kiranta da suna Bahar –al-Ahmar, Turawa kuma suke kiranta da suna “Red sea” wato jar teku kenan a hausance, ta samo wannan suna ne sakamakon yanayin jaja-jaja na tsaunukan da suke wannan yan yanki inda Bahar-maliyan take.

Wani shahararren marubuci da ake kira da suna Mr E.M.Foster,ya bayyana cewa,tun tale-tale matafiya da yan safara wadanda suke ratsawa ta wannan teku, suka sa mata wannan suna “Red sea” ko kuma “Bahar-ahmar’’.

Idan aka koma ga bayanan da ke kunshe a kundayen tattara bayanan abubuwan Duniya kuwa,kundin tarrabayanan abubuwan duniya na kasar Birtaniya, ya kawo nasa ra’ayin sabanin wannan, inda ya ke cewa wannan suna na “Red sea’’ da Turawa suke kiran tekun Bahar –maliya da shi, ba saboda yanayin jaja-jaja na tsaunuka bane, a’a, sakamakon yawan gamsakuka da take kewaye da gabar tekun wanda idan rana ta haska sai ta mai da tekun ta rinka daukar launin jaja-jaja ruwan dorawa-dorawa,wannan shine dalilin dayasa ake kiran ta da suna “Red sea’’ wato Jar-teku.

Ta bangaren masana ilimin kimiyya kuwa, sakamakon nazarin da wasu likitoci da kuma masana ilimin tarihi da halittun cikin ruwa suka gudanar,a shekarar 1646. Wani shahararren likita kuma marubucin litattafan turanci da ake kira da suna Sir Thomas Brown ne ya bayyana a cikin littafinsa cewa, wani masani akan halittun Ruwan-teku da ake kira da suna Sir Walter Raleigh, ya na kan raayin cewa, Bahar-maliya dai teku ce da take da launuka daban-daban, ya danganta da bangaren da mutum ya ke kallonta. Sir Raleigh ya ci gabada bayyana cewa nazarin da yayi game da tekun baharmaliya ya tabbatar masa da cewar wannan teku tana da launuka daban-daban. Wani bangaren kore ne fatau,wani bangaren kuma zaka ganshi fari ne da ruwan dorawa-dorawa, wani gurimma ka gan shi shudi-shudi. Sabodahaka kalar kowanne bangare na tekun ta dangantane da yanayin yashi ko kuma lakar da take acan kar kashin kasa.

To sai dai duk dacewar wannan amsa da muka baiwa Malam Bagudu bata tabbatar da takamaiman kalar tekun Bahar-maliya ba,amma dai gabakidayan bayanan suna bada amsar tambayar da cewa a’a, ruwan tekun Bahar-maliya ba ja ba ne.