1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubale game da yaki da cutar Kwalara a Yemen

Zainab Mohammed Abubakar
November 10, 2017

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta yi gargadin cewar toshe hanyoyin shigar da kayan agaji cikin Yemen da Saudiyya ta jagoranci yi na barazana ga kokarin shawo kan cutar Kwalara a kasar.

https://p.dw.com/p/2nQyQ
Jemen Cholera
Hoto: Getty Images/M.Huwais

Mutane sama da dubu da tara ne suka kamu da cutar kwalera a Yemen tun bayan sake barkewar cutar a a watan Afrilun da ya gabata. Tuni dai mutane sama da dubu biyu ne suka rasa rayukansu daga cututtuka da ke da alaka da rashin ruwa mai kyau saboda gurbacewar ruwa da muhalli a yankunan da ake cigaba da fada. Alluran riga kafi na gama-gari da aka gudanar a 'yan kwanakin nan sun taimaka wajen rage yaduwar cutar tsakanin jama'a. Sai dai toshe hanyoyin shigar da kayayyakin agaji musamman magunguna da abinci zuwa cikin Yemen da dakarun kawance da Saudiyya ke wa jagoranci suka yi na neman ta'azzara halin da kasar ke ci.

Unterernährung im Jemen
Rashin magunguna na baraza ga yaki da cutar Kwalara a YemenHoto: Getty Images/B. Stirton

Shugaban kungiyar likitocin kasa da kasa wato Medecins Sans Frontiers a kasar ta Yemen Justin Armstrong ya ce miliyoyin al'ummar kasar na dogaro ne da tallafin magunguna da abinci mai gina jiki da ruwan sha da suke samu daga kungiyoyin agaji na kasa da kasa inda ya ke cewar "tasirin hakan tuni ya bayyana, miliyoyi  basu da abinci mai gina jiki ko kuma ruwan sha mai tsabta. Toshe hanyoyin shigar da abinci zuwa kasar zai kara sanya rayuwa ta ta'azzara tsakanin al'umarta".

A wannan Alhamis din ce Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin agaji guda ashirin suka sanar da cewar mayakan hadaka da Saudiyya ke wa jagoranci sun toshe karin hanyoyin shigara da kayan agaji zuwa cikin Yemen da yaki ya daidaita kuma miliyoyin mutane ke bukatar agajin gaggawa na abinci. Shugaban hukumar agaji na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira OCHA reshen Yemen George Khoury ya shaidar da cewar wannan mataki da kasashen kawance suka dauka zai jefa rayukan mutane miliyan bakawai cikin halin kaka ni kayi. Ita ma hukumar kula da yara kanana ta UNICEF ta bayyana damuwarta dangane da hali na tagayyara da yara kanana ke ciki wadanda su ne cututtuka da yunwa ya fi addaba.