1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen dake gaban tsoffin shugabanni a Africa

January 11, 2006
https://p.dw.com/p/BvCk

Mutumin da ake kallon sa a matsayin dattijo a nahiyar Africa, wato Mr Nelson Mandela yace tsoffin shugabanni a kasashen Africa na da muhimmiyar rawar daya kamata su taka wajen wanzuwar zaman lafiya da lumana a nahiyar.

Za´a samu cimma wannan burin ne a cewar Mr Mandela, idan tsoffin shugabannin suka kara kaimi wajen shiga tsakanin sasanta rikice rikice da tashe tashen hankula da wasu kasashe a nahiyar ke fuskanta.

Mr Mandela, wanda ya fadi hakan a lokacin taron tsoffin shugabannin kasashen na Africa a birnin Maputo na kasar Mozanmbique a yau laraba, ya ci gaba da cewa shugabannin ka iya kasancewa nahiyar gwadaben fita daga kangi na fatara don bunkasar tattalin arziki , ta hanyar janyo hankalin kasashe da suka ci gaba a duniya saka hannun jari a kasashen nahiyar.

Wannan dai dandali na tattaunawar tsoffin shugabannin, bayanai sun nunar da cewa tsohon shugaban kasar ta Mozambique ne, wato Joaquim Chissano ya kirkiro shi bayan yayi murabus shekara daya data gabata.