1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalensufurin Jiragen sama a Najeriya

October 21, 2016

Masana zirga zirgar Jiragen sama a Najeriya sun yi tsokaci game da rashin ingancin filayen saukar jiragen sama a kasar tare da nazarin hanyoyin samun mafita.

https://p.dw.com/p/2RXig
Nigeria Flughafen Lagos Archivbild 2007
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Taron masana sufurin Jiragen saman kasar ya hado fittatun masana ta fuskar zirga zirgar jiragen sama a Najeriya, jam'ain tsaro da ma wasu jami'an rundunar sojin sama, inda suka kaifafa basira game da hanyoyin magance hadarurukan jiragen sama, da ma batun samar da ingantattun kayan aiki a daukaccin filayen jiragen saman Najeriya, da kuma horas da ma‘aikata dake fanoni daban daban a fanin zirga zirgar jiragen saman.

Malam Bello Abdulmuminu, wani masani ne kan sha'anin sufurin Jiragen sama, yace rashin kulawa da Jiragen ita ce babbar matsala, amma ba wai karancin Jiragen sama a Najeriya ba.

Wata matsalar a cewar Malam Abdulmuminu ita ce rashin kwarewar masu bada hanu ga Jarage a filayen saukar Jiragen sama da kuma rashin ingancin kayyan aiki a manyan filayen jiragen saman na Najeriya.

Türkei Airbus A321 Turkish Airlines
Hoto: picture-alliance/blickwinkel/McPhoto

 Shi ma a mukalar da ya gabatar, Mr Victor Eyamu, daya daga cikin jami'an kungiyar maikatan dake kula da zirga zirgar jiragen saman a Najeriya yace ba sai an sami hatsarin jirgin sama ba kafin a fara samar da kayyayakin aiki a filayen jiragen sama ba, ya kamata tun kafin wani abu ya auku, hukumomin da abin ya shafa sun himmatu wajen samar da ingantattun kayan aiki domin rashin yin hakan tamkar nuna halin ko oho da rayukan jama’a

Mahalarta taron sun yi dogon nazari game da irin mutanen da akan dauka aiki a wannan fanni na sufuri, tare ma da wadanda suka ce basu da wata kwarewa inda akan bari su tafiyar da ayyuka duk da irin hadarin dake tattare da yin haka.