1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Farin cikin komawa makaranta a fadin kasa

September 5, 2017

Makarantu a yankin Kamaru da ke magana da Ingilishi sun bi sahun takwarorinsu na bangaren Faransa wajen komawa makaranta a lokacin da gwamnati ta tsara.

https://p.dw.com/p/2jNRX
Kenia Schulmädchen aus dem Thomas Barnados Kinderheim in Nairobi
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com

A Jamuhuriyar Kamaru a ranar hudu ga watan Satumba dalibai a fadin kasar suka koma makaranta, matakin da ke zama abin faranta rai ga iyayen yara ganin yadda aka yi ta faman yaje-yajen aiki da ya sanya karatun yara cikin garari musamman a yankin da ke magana da harshen Ingilishi.

Wasu makarantu na yankin kasar da ke magana da harshen na Ingilishi sun bi sahun takwarorinsu na bangaren Faransanci wajen komawa makaranta a lokacin da gwamnati ta tsara. Wannan ya biyon bayan sako daukacin masu fafutukar kwato wa yankin Anglophone din mutunci a hannun gwamnati.

Kamerun Schulunterreicht in Moho
Sai dai a wasu yankuna kamar a Moho, wani kauye da ke jihar Arewa mai Nisa, yara na karatu ne karkashin bishiya saboda rashin azuzuwaHoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Jama'a da dama cikin jihohi Kudu maso Yamma da Arewa maso Yamma sun fito kan tituna don nuna farin cikinsu tare kuma da nuna goyon bayansu ga komawar yara makarantun gwamnati da ma masu zaman kansu.

Dalibai sama da miliyan hudu ne a fadin kasar ta Kamaru suka koma makaranta. Cikinsu akwai na sakandare da firamare sai kuma na 'yan nasare, inda wasu sabbin shiga makarantun musamman ma kananan yara suka rika kuka saboda sabon yanayi da suka shiga ciki. Sai dai ba dukka dalibai ne suka koma maranta ba.