1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Harin bam a wata kasuwa

Yusuf BalaFebruary 19, 2016

Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da ya yi sanadi na rayukan mutane da dama a Arewacin na Kamaru, harin da Boko Haram ta saba Kai irinsa a kasar.

https://p.dw.com/p/1HycY
Kamerun Anschlag in Maroua
Yankin da aka kai harin bam a Arewacin KamaruHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Wasu tagwayen hare-haren bama-bamai a wata kasuwa a lardin Meme da ke a Arewacin Kamaru ya yi sanadi na rayukan mutane 19, yayin da wasu 50 suka samu raunika kamar yadda mazauna yankin suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da ya yi sanadi na rayukan mutane da dama a Arewacin na Kamaru da ke ganin yawaitar ayyukan ta'addanci daga kungiyar Boko Haram mai sansani a Najeriya.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki nauyin wannan kai hari da aka saba ganin kungiyar ta Boko Haram na kaishi.