1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Mutane 14 suka mutu a harin Waza

Salissou Boukari
July 13, 2017

Tawagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a birnin Waza da ke yankin Arewa mai nisa na kasar Kamaru sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 14 tare da raunata wasu 30.

https://p.dw.com/p/2gTLp
Kamerun Anschlag in Maroua
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Harin dai ya wakana ne a birnin Waza da ke yankin Arewa mai nisa na kasar ta Kamaru, yankin da ake yawan fuskantar hare-haren 'yan ta'adda na kungiyar Boko Haram. Daya daga cikin mahukuntan birnin na Waza, da ke tsakanin birnin Maroua da Kousseri da ke iyaka da Najeriya wanda bai so a bayyana sunan shi ba ya tabbatar da mutuwar mutane 16 cikinsu 14 fararan hulla da kuma 'yan kunar bakin waken su biyu.

'Yan ta'addan biyu dai sun shiga wani wuri ne da ake samun cinkoson jama'a, inda ake da wuraran cin abinci da na buga waya, da ma wuraran sayar da kayan sanyi, kuma su ka tawartsa kansu a wurin. Majiyar na cewa wasu daga cikin wadanda suka samu raunukan na cikin mawuycin hali.