1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane 1,500

November 16, 2016

Kungiyar sa ido kan harkokin tsaro a duniya watau International Crisis Group, ta ce mutane fiye da dubu 150 sun rasa rayukansu kana ya tilastawa wasu mutane dubu 78 yin gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2SmYs
Kamerun Soldaten Anti Boko Haram
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Chimtom

Kungiyar sa idon kan harkokin tsaron ta International Crisis Group a Kamaru ta ce ko da yake mahukuntan na Kamaru suna samun nasara a yakin da suke yi da Boko Haram musamman a lardin Arewa mai nisa, har yanzu ba'a kawar da matsalolin da ke zama taki ga rikicin ba. Wadannan matsaloli a cewar Hans De Marie Heungoup na kungiyar ta ICG a Kamaru sun hada da matsaloli na talauci abin da yace kungiyar ta Boko Haram ke amfani da wannan dama wajen jan ra'ayin matasa ta hanyar yi musu dan hasafi:

Kamerun Anschlag in Maroua
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

"Abin da yake a zahiri dai shi ne cewa kantar talauci a arewacin Kamaru ya bada damar shigar 'yan Boko Haram tare da daukar mayaka a tsakanin al'umma musamman a yankunan kan iyaka kamar Fotokol da Kolo fata da sauran yankuna na kan iyakar."

Ya ce idan aka yi lakari, za'a ga cewa Boko Haram, sannu a hankali ta shiga kasar Kamaru daga watan janairu na shekarar 2014 inda ta ke yin barazana ga hukumomi har ma da gargadin kasar a kan kada ta sa kanta a rikicin da kungiyar ke yi da Najeriya. Sai dai kuma bayan da kasar ta Kamaru ta zafafa kai farmaki kan kungiyar ta Boko Haram, kungiyar ta ce ta ja daga kuma ta shiga yaki da kamarun ta hanyar kai hare hare ba kakkautawa.