1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Sojoji sun yi wa garin Buea kawanya

Suleiman Babayo AH
October 2, 2017

Jami'an tsaro na ci gaba da yin sintiri a garin Buea inda 'yan aware na kudu maso gabashin Kamaru ke neman ballewa. Yanzu haka dai darurruwan mutanen da ke zaune a garin sun tsere saboda fargaban tashin hankali.

https://p.dw.com/p/2l7FP
Kamerun - Proteste
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Daya daga cikin mutanen da suka fito daga wannan yanki na Kamaru da ake magana da harshen Ingilishi shi ne jaroran 'yan adawa na kasar John Fru Ndi, wanda kuma ya yi hira da wannan tasha ta DW wanda ya ce hukumomin Kamarun sun yi watsi da yankin. John Fru Ndi shugaban jam'iyyar SDF kana jagoran 'yan adawa na Kamaru wanda ya fito daga yankin da ake magana da harshen Ingilishi ya danganta matsalolin da ake ciki da yadda shugaba Paul Biya na kasar ta Kamaru ke nuna ko'in kula game da matsalolin da kasar ke ciki, kuma ga abin da Fru Ndi yake cewa bisa wannan riciki a yankin da ake magana da harshen na Ingilishi."Matsalolin yankin da ake magana da harshen Ingilishi shugaba Biya ya kirkiro kuma ya aiwatar, saboda matsalolin da suke Kamaru shi Paul Biya ba ya duba su ko kadan. Lokacin da rikicin ya barke na ga yara kananan da suka shiga, sai na samu shugaba Biya na shaida masa cewa ya kamata ya yi wani abu domin lamarin ya wuce yadda aka saba gani,na shaida wa  Biya wannan hadari ga kasa, amma bai kula ba." Wani salon  gwagwarmayar da yankin  ya dauka shi ne neman aware domin dara Kamaru gida biyu, kamar yadda 'yan gwagwarmayar  masu magana da harshen Ingilishi ke bukata, wanda kuma bisa ga dukkan alamun John Fru Ndi bai nuna kin amincewa ba da haka.

John Fru Ndi
John Fru Ndi jagoran 'yan adawa na KamaruHoto: M. Happi