1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kameni ya ýi watsi da hukuncin mdd akan Iran

January 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuV3
Wolfgang Huber shugaban majalisar cocin Evangelika a Jamus
Wolfgang Huber shugaban majalisar cocin Evangelika a JamusHoto: AP

Shugaban addini na kasar Iran,Ayatolla Ali Khamene yayi watsi da da zartarwar komitin sulhun mdd dangane da hukunta kasar sakamakon shirin nuclearn ta.Khameni yace Iran bazata taba watsi da yancinta na nuclear ba.Wadannan kalamai nasa da yayi yau a bainar jamaa na zama na farkon irinsa ,bayan da komitin sulhun mdd ya zartar da kakabawa Iran din takunkumi a ranar 23 ga watan Disamban daya gabata ,saboda taki dakatar da bunkasa sinadran Atom dinta.Kasashen turai dai suna fuskantar barazana sakamakon zargin da sukewa Iran din na sarrafa makamin nuclear.Tehran dai tayi watsi da wannan zargi da ake mata,dacewa sarrafa sinadran ta na Atom bashi da wata muguwar manufa,face samarwa alummar kasar ingantaccen wutan lantarki.