1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kammala yakin neman zabe a faransa

April 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuNP

Yan takarar kujerar shugabancin kasar faransa guda 12,sun kammala kampagn na yakin neman zabensu a yau,domin neman goyon bayan masu kada kuriu a zagaye na farkon zaben dazai gudana a ranar lahadi a wannan kasa.

Dan takara Nicolas Sarkozy da sauran abikan takararsa dai sunyi alkawarin kawo sauyi ,saidai dukkanninsu nada sabanin raayi dangane da yadda zasu cimma wannan buri ,musamman bisa laakari da matsalar karuwar rashin aikinyi da basussuka da ake bin kasar ,da kuma irin rigingimu da ake fuskanta a unguwannin baki,wanda ya haifar da tarzoma a shekarata 2005.Bisa ga kuriar jin raayin jamaa da aka gudanar dai,Mr Sarkozy shine ke jagoranci ,ayayinda zaa fafata tsakanin Segolene Royal da Francois Bayrou a mataki na biyu, a zagaye na biyun wannan zabe da akesaran zai gudana a ranar 6 ga watan mayu mai kamawa.