1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamo furzunonin Nigeria da suka tsere

September 12, 2010

Sojojinn Nigeria sun kamo wasu daga cikin furzunonin da suka arce daga gidan yarin Bauchi.

https://p.dw.com/p/PAI8
Sojan Nigeria a lokacin bincikeHoto: AP

Jami'an tsaron tarayyar Nigeria sun yi nasarar tsafko biyu daga cikin furzunonin da suka arce bayan da wasu gungun 'yan takife suka kai hari a gidan yarin Bauchi da ke arewacin ƙasar. Wani da ke magana da yawun rundunar sojan jihar plateau wato leftenan-kanal Kingsley Umoh ya ce sun kama mutanen ne tun ranar juma'a a lokacin da suka nufin birnin Jos.

 Ko da shi dai furzunonin biyu sun bayyana cewa ba su da alaka da ƙungiyar Boko haram, amma kuma dukkaninsu  an ɗauresu ne bisa laifin da ke da alaka da kisan kai,  da kuma ayyukan da ke da nasaba da tayar da zaune tsaye.

Furzunoni da dama ne dai jami'an Nigeria suka yi nasarar mayar da su gidan yarin na Bauchi baya ga mutane 120 da suka koma don raɗin kansu a gidan yarin. furzunoni 7 32 ƙungiyar ta Boko haram ta yi sanadiyar arcewansu ciki kuwa har da 'yayanta 150 da ake ci gaba da nema ruwa a jallo.

 Mutane huɗu ne dai suka rasa rayukansu a artabun da ya wakana a makon da ya gabata a lokacin da 'yan bokon haram suka kai wannan harin a Bauchi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Ahmed Tijjani Lawal