1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamun ludayin Buhari cikin shekaru biyu na mulki

May 29, 2017

Bayan share rabin wa'adin mulkin gwamnatin Muhammadu Buhari, al’ummar tarrayar Najeriyar na maida martini dangane da shekarun biyu da ke zaman zakaran gwajin dafi a fannin tsaro da cin hanci da tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/2dlBx
Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

A cikin fata da babban buri ne miliyoyin al'ummar tarrayar Najeriya suka zabi canji a karon farko, abin da ya haifar da sabuwar gwamnatin Buhari ta 'yan canji shekaru biyun da suka gabata.  Gwamnatin dai ta zo ne a cikin manyan alkawura guda uku na sake tabbatar da tsaron da ya nemi ya rushe a kasar da kawo karshen annobar hanci, sannan da uwa uba inganta tattalin arziki. Duk da cewar babu bukukuwan al'ada a lokaci irin wannan, bayan shekaru biyu dai a fadar kakakin gwamnatin Malam Garba Shehu gwamnatin ta darma sa'a a bisa alkawuran data dauka tsakaninta da al'ummar tarrayar Najeriya a halin yanzu.

An ga fari an ga baki a shekarun biyu sakamakon nasarori a cikin raki na ta'adancin tarrayar Najeriya, Sannan da kokarin kai cin hanci ya zuwa gidan tarihi. Sai dai kuma tattalin arziki ya bada kasar sakamakon faduwar farashin man fetur dama ayyuka na tsagerun yankin Niger Delta. Dr Garba Umar Kari da ke zaman masanin harkokin kasar ta Najeriyar, ya ce babu yabo babu fallasa ga gwamnatin MUhammadu Buhari a shekaru biyu. 

Nigeria Präsident Muhammadu Buhari und die freigelassenen Chibok-Mädchen in Abuja
Buhari ya yaki Boko Haram tare da kubutar da Wasu 'yan matan ChibokHoto: Reuters/Presidential Office/B. Omoboriowo

Sai dai kuma in har gwamnatin ba ta kai ga iya biyan dimbin fatan da ke a tsakanin al'umma a kasar ba, ra'ayi ya zo kusan daya a bisa kokarin gwamnatin wajen tunkarar lamura na kasar, a cewar Peter Inalegwu da ke zaman wani mazauni na Abuja. Amma kuma a tunanin Abdulkarim Dayyabu da ke sharhi a bisa lamarin cikin kasar dai babu hujja ta hukunci ga Buhari da share kusan rabin wa'adin na shekaru biyu yana kai kawo a tsakanin Abuja ya zuwa birnin London da nufin neman magani.