1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Kano: Na'urar samar da man disel na itaciyar zugu

November 9, 2016

A Najeriya wani matashi ami suna Kamilu Yahaya ya kirkiro da wata na'ura ta samar da man disel daga ganyayyakin fidda zugu ko bini da zugu.

https://p.dw.com/p/2SPkH
Nigeria Kano Kamilu Yahaya Biodiesel Produktion
Hoto: DW/K. Sani

A yayin da gwamnatin Najeriya take ta kokarin fadada harkokin samar da makamashi ,yanzu haka an sami wani matashi mai suna Kamilu Yahaya wanda yake dan asalin jihar Kano ne daya kirkiro da wata na’urar samar da man disel daga ganyayyakin fidda zugu ko kuma bini daga zugu wato (Jatropha) a turance wanda aka fara amfani dashi a jihar Legos a karon farko.

 

Nigeria Kano Kamilu Yahaya Biodiesel Produktion
Hoto: DW/K. Sani

Malam Kamilu Yahaya wanda yake matashi ne mai hazaka ya fara nuna matikar sha’awar bibiyar harkokin fasaha ne tun yana karamin yaro, a inda ya dunga nuna juriya tare da duba hanyoyin da zai amfanar da jama’a ta hanyar fasahar da Allah ya huwace masa a yayin da kamar ragowar matasan da ke da fasahar kawo sauyi da cigaban jama’a bai sami zarafin tafiya wata babbar makaranta ba,To sai dai labarin Kamilu na kwashe shekaru sama da 11 na nazarin yadda zai samar da ita wannan na’urar wacce ke tace mai daga ganyen fidda zugu irin su disel da sauran su kamar dai yadda ya yi karin bayani.

 

" Danyan man da muke aiki da shi ba irin wanda ake hakowa ba ne, danyan mai ne daga tsurrai. Kuma mu fara aikin shi tun muna matsawa da abu na matsawa har muka gano matsa shi da inji har zuwa lokacin da za a fiddo da man a sarrafa shi a fitar da disel daga cikinsa, sannan ka samar da makamashin wuta da kuma takin zamani da kuma sabulu"

Tuni dai wani kamfani mai suna Mopan a Kano ya soma aiki da wannan inji mai aiki da man disel na itaciyar bini da zugu.