1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin abinci da magunguna a birnin Fallouja

Salissou BoukariFebruary 2, 2016

Gwamnan jihar Anbar a kasar Iraki ya yi kira ga sojojin kawance masu yakar 'yan IS da kasar Amirka ke wa jagoranci da su jefo abinci da magunguna ta sama a Fallouja.

https://p.dw.com/p/1Ho5f
Irak Soldaten befreien Zivilsten in Ramadi
Hoto: Reuters

Birnin na Fallouja dai da ke a nisan kilomita a kalla 50 a Yammacin birnin Bagadaza, na a hannun 'yan kungiyar IS ne amma kuma sojojin gwamnatin ta Iraki sun yi masa kawanya. A cewar Gwamnan jihar ta Anbar Sohaïb Al-Raoui a halin yanzu dai babu wasu dakaru da kan iya shiga cikin birnin domin kula da shigar da kayan agaji, don haka sai dai a jefo ta sama. Suma dai wasu mazauna birnin na Fallouja da aka tuntuba ta wayar tarho sun ce al'umma na fuskantar babban karancin kayayakin abinci, da magungunna da kuma man fetir na zirga-zirga.