1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin haihuwa na addabar kasashen Turai

January 23, 2006

Halin da ke samu na karancin haihuwa a nan nahiyar Turai na ci wa humomin kasashen nahiyar tuwo a kwarya. Game da haka ne dai gidan rediyon Deutsche Welle da gidauniyar nan ta Betelsmann suka shirya wani taron bita a kan wannan batun abirnin Berlin.

https://p.dw.com/p/BvTy
Jama'ar Turai na ta kara tsufa, yayin da haihuwa ke komawa baya.
Jama'ar Turai na ta kara tsufa, yayin da haihuwa ke komawa baya.Hoto: AP

Kiyasin da kafofin kula da tsarin zaman al’umma da yawan jama’a a nan Jamus suka yi, na nuna cewa, an ata kara samun yawan tsoffin mutane a nan kasar, yayin da yawan matasa kuma, sai kara komawa baya yake yi. Bisa alkaluman baya-bayan nan da aka buga dai, kafin nan da shekara ta 2050, ko wani bajamushe daya bisa uku, zai kasance ne mai shekaru 60 da haihuwa. Hakan kuwa, inji masana fannin halin zaman jama’a, zai sami wani gagarumin angizo a kan halin rayuwa a nan Jamus. Mai yiwuwa a wayi gari, ana karancin ma’aikata, maimakon yawan marasa aikin yi da ake ta fama da su a halin yanzu. Dalilin wannan sauyin da ake hasashen samu dai, shi ne karancin haihuwa da ake ta samu a duk fadin tarayya. A nan Turai dai, alkaluma na nuna cewa, idan aka raba duk yaran da ake da su a halin yanzu ga duk mata, to ko wace mace a Jamus za ta sami da daya ne da digo uku, a Faransa kuma da daya da digo 9. Akwai dai dalilai da dama da ke janyo wannan halin da ake ciki, inji Francois Héran, daraktan cibiyar nazarin yawan al’umma ta kasar Faransa:-

„Halin da ake ciki dai na da jibinta ne da manufofin siyasa na iyalai, amma ba wannan kadai ba. Akwai kuma jerin wasu ababa da ake la’akari da su, kamarsu mazauni da makarantun horad da yara.“

A nan Jamus dai, an dade ana kauce wa tattaunawa kan wannan batun, inji Rudolf Herweck na ma’aikatar kula da jin dadin jama’a. Sai bayan shekara ta 2003 ne aka fara canza ra’ayi kan yadda all’amura suke a zahiri. Ya kara da cewa:-

„Sabuwar manufar da muka sanya a gaba dai na dauke da sakon fadakad da jama’a ne kan cewa, kudi kawai ba zai iya magance mana matsalarmu ba. Ban da kudi muna bukatar lokaci da kuma kafofin kula da sassa daban-daban na rayuwa. Gwamnati kawai ba za ta iya tafiyad da wannan siyasar ita kadai ba. Muna bukatar gudummuwar jama’a don mu iya aiwatad da duk manufofin.“

Manazarta a fannonin tattalin arziki da na tsarin yawan al’umma dai na ganin cewa, sauyin da aka samu a halin rayuwa a nan Turai da kuma burin da jama’a suka sanya a gaba ne ke janyo wannan halin da ake ciki na rashin yawan haihuwa.

A kasashen da ke wajen Turai, kamar dai a nahiyar Afirka ko kuma a kasashen musulmi, ba haka lamarin yake ba. Amma duk da haka, an sami canje-canje a kasashe kamarsu Aljeriya da Marokko da kuma Tunesiya a cikin kusan shekaru 20 da suka wuce, injni Francois Héran, daraktan cibiyar nazarin halin rayuwa da yawan jama’a na kasar Faransa:-

„A farkon shekarun 1970 dai, alkaluma na nuna cewa, a ksasashen na arewacin Afirka, ko wace mace na samun yara bakwaine, a takaice. Amma a yau, al’amura sun canza. A kasar Aljeriya, ko wace mace na haifar yara 2 ne da digo 5, a Maroko kuma yara biyu da digo 3, yayin da ragowar ta fi tsamari a kasar Tunesiya, inda ko wace mace a yanzu ke haifar yara 2 da digo daya. Wannan sauyin kuwa, a cikin dan gajeren lokaci aka same shi. A wadannan kasashen dai, mun lura da cewa, yayin da mata ke aure da shekaru 15 a 1970, a halin yanzu ba sa aure sai sun bai wa shekarru 28 baya.“

Manyan dalilan da ke janyo hakan kuwa, inji Héran, sun hada ne da karin yawan mata masu ilimi mai zurfi da aka samu. Amma wannan salon, bai yadu zuwa ksashen Afirka kudu da Sahara ba tukuna. A kasashe kamarsu Niger, da Mali da Uganda, har ila yau ko wace mace na haifar a kalla yara 7.