1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa noman shinkafa a Najeriya da Nijar

January 4, 2017

Manoman kasar na bukatar samun karin tallafi domin inganta noman shinkafar.

https://p.dw.com/p/2VGsg
Traditionelle Landwirtschaft
Hoto: Estácio Valoi

A Nijar Hadin gwiwar kungiyoyin manoman shinkafa da ke Niamey da Tillabery sun  koka da rashin samun duk wani tallafi daga gwamnati ta yanda za su samun sukunin noman shinkafar da ma wadatar da ita ga kasar domin rage  shigowa da ita daga waje. Manoman shinkafar sun ce sunma da matsaloli barkatai da suka hada da rashin ingantacen irin shinkafa na zamani  da rashin kayan noma musamman ma injinan ban ruwa da na takin zamani  da magungunan kashe kwari.Hakan kuwa na faruwa ne duk da irin matakin da gwamnatin ta dauka a karkashin shirinta na dan Nijar ya ciyar da dan Nijar wajen habaka harkar noman.Manoman na shinkafa sun yi gargadin cewar za u bi duk hanyoyin da suka dace na samun tallafin daga gwamnatin domin inganta noman shinkafa a Nijar.