1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karo na 3 a ƙarshen mako an sake kai harin ƙunar baƙin wake a Pakistan

July 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuGJ
Wani dan kunar bakin wake ya halaka akalla mutane 12 sannan ya jiwa wasu 20 rauni a wata cibiyar daukar ´yan sanda aiki dake yankin arewa maso yamacin kasar Pakistan. Wannan harin dai shi ne irinsa na 3 da aka kai a yankin a karshen wannan mako. Da farko wasu ´yan takife da ake zargi ´ya´yan kungiyar Al-Qaida ne da na Taliban sun kai tagwayen hare haren kunar bakin wake inda suka halaka mutane 17 ciki har da sojoji 11 a wani abin da ke zama daukar fansa ga murkushe masallacin Lal Masjid na birnin Islambad da gwamnati ta yi. A jiya asabar wani dan kunar bakin wake dauke da bama-bamai a cikin mota ya afkawa ayarin motocin jami´an tsaro inda ya kashe akalla mutane 14 a wannan yanki dake kusa da kan iyakar Pakistan da Afghanistan.