1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen shekara a Zimbabwe

Zainab MohammedDecember 25, 2008

Hali Mawuyaci da Zimbabwe ke ciki

https://p.dw.com/p/GN1e
Desmond Tutu.Hoto: AP Photo

Ƙasar Zimbabwe dake yankin kudancin Afrika dai na bukin chrismetin wannan shekara cikin hali mawuyaci na durkushewar tattalin arziki, baya ga matsalar yunwa da ɓarkewar cutar kwalera.

"Zan jaddada cewar, kada mu nisanta kammu da ɓangaren waɗanda ke fama da wahalhalu na rayuwa". Ach bishop Desmond Tutu na Afrika ta kudu kenan, ke tsokaci dangane da mawuyacin hali da al'ummomin Zimbabwe ke ciki.

EU Sondergipfel in Brüssel Jose Manuel Barroso
Jose Manuel BarrosoHoto: AP

Masu lura da alamuran yau da kullun sun bayyana wannan ƙasa da kasancewa cikin halin kaka nikayi na rayuwa adaidai wannan lokaci da ake shirin shiga sabuwar shekara.

Akwai kimanin 'Yan zimbabwe million 5 dake fama da matsanancin yunwa,ayayinda kididdiga yayi nuni dacewar mutane dubu 24 ne ke fama da cutar kwalera, bayan wasu dubu 12 da suka rasa rayukansu da annobar cutar.

Acewar Ach bishop Tutu wannan gazawace a bangaren magabata..

"Ina ganin mun gaza sauke nauyin daya rataya a wuyanmu na rikon amanar al'umma,domin muna yi kamar mutane basa cikin wahala,wane irin mawuyacin hali zasu shiga, wanda zai sa mu nunawa Mugabe cewar Lokacin shi ya kare?

Amurka da kungiyar tarayyar turai EU dai na nanata kira ga shugaba Robert Mugabe mai shekaru 84 da haihuwa daya sauka daga karagar mulki. Kamar yadda shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar tarayyar turai Jose Manuel Barroso yayi nuni dashi.

"Dukanni wakilan kasashe 27 na turai sun amince dacewar, lokaci yayi da mugabe zaiyi murabus daga karagar Mulki"

Präsident Mugabe bei Wahlkampfauftritt in Chitungwiza
Robert MugabeHoto: picture-alliance/ dpa

To sai dai duk wadannan korafe korafe da kiraye kiraye a bangaren kasashen duniya da hukumomi sun kasance tamkar wake ne a bangaren shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe,mutumin da ke shugabantar wannan kasa dake yankin kudancin Afrika tun bayan data samu mulki daga turawan mulkin mallaka na Britaniya..

"Mugabe yace Su Su wanene da zasu zartar mana wadanda suka cancanci shiga ko kuma kasancewa a gwamnati,gwamnatimmu"

A tsakiyar watan Satumba nedai aka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka,wanda saɓani kan madafan iko ya haifar da rashin kafuwar wannan gwamnati.

A yanzu da aka doshi sabuwar shekara dai, har yanzu al'ummar Zimbabwen na fama da yunwa,ga durkushewar tattalin arziki. Kana ba tare da tallafin asusun kula da lafiyara ta UNICEF,da ƙungiyar agajin ƙasa da ƙasa ta Red Kros,da ƙungiyar kula da lafiya ta Mdd ba, lamarin halin da ake ciki na cutar kwalera zai iya tsananta, wanda babu wanda ke fatan hakan, sai dai muce Allah ya kiyaye.