1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar mata 'yan takara a kasar Lebanon

Salissou Boukari MNA
March 7, 2018

Rahotanni daga kasar Lebanon na cewa, 'yan takara kusan dubu ne, cikinsu mata sama da 100, za su fafata a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da zai gudana a farkon watan Mayu mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2ts4Z
Bildergalerie Hisbollah-Anhänger im Nahen Osten Libanon
Hoto: Getty Images/AFP/R. Haidar

Wannan shi ne karo na farko tun yau da shekaru tara da suka gabata da kasar ta Lebanon za ta gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a cewar kamfanin dillancin labaran kasar na ANI.

Akalla 'yan takara 976 ne za su nemi kujeru 128 na 'yan majalisar dokokin kasar, cikinsu mata 111. A zaben da ya gudana na shekara ta 2009, mata 'yan takara 12 ne kacal aka samu daga cikin 'yan takara 706 a tsakanin masu neman kujerar ta 'yan majalisa.

Majalisar dokokin kasar ta Lebanon ta yi ta kara wa kanta wa'adi har sau uku, sakamakon matsalar tsaro, da kuma rikicin siyasa da ke da nasaba da rikicin da ake a makwabciyata kasar Siriya.