1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar yawan jamaa a duniya

March 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuPg

Wani rahoton MDD duniya akan yawan jamaa yace yawan jamaar duniya zai karu zuwa biliyan 9.2 haka kuma mutane yan shekaru 60 da haihuwa zai karu da ribi uku nan da 2050.

Sashen kula da yawan jamaa na majalisar yace ana sa ran yawan karuwar jamaar a kasashe matalauta musamman kasashe 50 mafiya talauci a duniya wadanda yanzu suke da mafi yawa na matasa.

A kasashe masu arzikin masaantu kuma rahoton yace akidar kin haihuwa da yanzu ya zama ruwan dare zai ci gaba,inda zaa samu raguwar yawan jamaa saboda babu wadanda zasu maye gurbin wadanda suke mutuwa.

Rahoton yace Nigeria Nijar Liberia India da Jamhuriyar Demokradiyar Kongo dama wasu kasashe zasu kasance dauke da mafiya yawa na karin mutane biliyan 2.5 da zaa samu nan da 2050.

Yawan jamaar kasar Nijar kuma inji rahoton zai nunka sau uku zuwa wannan lokaci.