1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karzai ya yi Allah Wadan nufin kona Al'qurani mai tsarki

September 10, 2010

Pasto Jones ya dakatar da manufarsa ta kona Al'qurani mai tsarki a gobe Asabar

https://p.dw.com/p/P8o6
Hoto: AP

Ayayin da al'ummomin Musulmi ke bukin Id-el fitr bayan kammala azumin watan Ramadan, shugaba Hamid Karzai na ƙasar Afganistan ya gargaɗi  Limamin kristan Amurkan nan da kada ya gwada kona Al'qurani mai tsarki kamar yadda ya ayyana yi. Shugaban Afgahnistan ɗin dai ya yi wannan gargaɗi ne a jawabinsa na al'ada a liyafar bayan saukowa daga sallar  Idi  wa manyan jami'an gwamnati a fadar gwamnati dake Kabul. A jiya alhamis ne dai Pasto Terry Jones na Florida dake Amurka, ya sanar da dakatar da aniyarsa ta kona ɗaruruwan Al'qurani, da cewar zai soke wannan muguwar manufa tasa ne kaɗai idan an fasa gina masallacin da ake shirin ginawa a birnin New York. Tuni dai shugabannin ƙasashen Duniya ke Allah wadan wannan batu, wanda ake ganin zai iya tozarta al'ummar Musulmi a daidai wannan lokaci da ake bukuwan Salla bayan kammala azumin watan Ramadan.

Mawallafiyya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu