1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin kuɗin 2008 kan yaƙin Iraqi

October 23, 2007
https://p.dw.com/p/C15s

Shugaban ƙasar Amurka George W Bush ya mika buƙatar Dala biliyan 46 ga majalisar dokoki domin amincewar ta na kuɗaɗen da zaá kashe wajen tafiyar da yaƙin Iraqi a shekarar 2008 Da yake gabatar da kasafin kudin ga yan majalisar, Bush yace yayi Imanin cewa wajibi ne a baiwa sojojin dukkanin taimako da gudunmawar da suke buƙata domin samun nasarar aikin su, yace wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan Amurka ta taimakawa sojojin ta yadda za su sami sukunin kare ƙasar da kuma alúmar ta. Bukatar ta ƙunshi kuɗaɗen tafiyar da da yaƙin Iraqi dana Afghanistan. Idan majalisar ta amince ta buƙatar zai kasance yaƙin Iraqin ya ci tsabar kuɗi fiye da dala miliyan dubu 750 tun bayan da Bush ya ƙaddamar yaƙi da ayyukan tarzoma bayan harin 11 ga watan Satumbar shekarar 2001.