1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Bulgeriya ta haramta sanya nikabi

September 30, 2016

Tara mai tsanani matar da aka samu so biyu da laifin sanya nikabi zata biya a Bulgeriya bayan da majalisar kasar ta haramta sanyashi a bainar jama'a. Alhali kashi 13% na al'ummar kasar Musulmi ne.

https://p.dw.com/p/2QmpI
Niederlande Holland Burka
Hoto: AP

Majalisar dokokin Bulgeriya ta amince da dokar da ta haramta sanya nikabi a bainan jama'a, matakin da ya sa ta zama kasar Turai ta uku da ta rungumi wannan tsari baya ga Faransa da Beljiyam. Dokar ta tanadi tarar Euro 100 ga duk matar da ta yi buris da ita, sai dai hukunci zai yi tsanani idan aka sami kowace mace da wannan laifi so biyu inda tarar zata iya kaiwa Euro 750.

Shekaru ukun da suka gabata ne Musulmin Bulgeriya wadanda suka kasance kashi 13% na al'uma suka fara sanya nikabi bayan da wani malami ya fara yada akidar salafiyanci. Amincewa da wannan dokar haramta sanya nikabi wadda ta zo wata gudana kafin zaben shugaban kasa, ta tayar da jijiyoyin waya na jam'iyyar MDL da ta kunshi dimbim Musulmi, inda ta zargi sauran shugabanni da amfani da siyasa wajen raba kawunan 'yan kasa.

Kungiyar Transparency International ta soki lamarin Bulgeriya inda cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Jumma'ar ta ce dokar haramta nikabi na daga cikin hauhawar wariya da kyama da ake fuskanta a kasar.