1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za ta rage sojoji 300,000

Yusuf BalaSeptember 3, 2015

Ya zuwa yanzu dakarun sojan kasar ta China su suka fi yawa cikin dakarun sojan kasashe a duniya inda adadinsu ya kai miliyan biyu da dubu dari uku.

https://p.dw.com/p/1GQOz
China Militärparade in Peking 70. Jahrestag Ende 2. Weltkrieg Bildergalerie
Dakarun sojan kasar ChinaHoto: Reuters/D. Sagolj

Mahukunta a kasar China sun bayyana cewa za su rage yawan dakarunsu da 300,000 a cewar shugaba Xi Jinping.

Ya zuwa yanzu dakarun sojan kasar ta China su suka fi yawa cikin dakarun sojan kasashe a duniya inda adadinsu ya kai miliyan biyu da dubu dari uku. Shugaba Jinping ya bayyana cewa akwai bukatar zaman lafiya ya ci gaba da dorewa a duniya, shugaban ya bayyana haka bayan da kasar ta gudanar da gagarumin faretin soja a bikin tunawa da shekaru saba'in da kasar ta yi bayan ta samu nasara a kan kasar Japan a karshen yakin duniya na biyu.

Yayin wannan gagarumin biki dai da ya sami mahalarta na shugabannin wasu kasashe abokan China a dandalin Tiananmen da ke a birnin Beijing, kasar ta China ta sake nuna irin karfin makamai da take dasu, hakan kuma na zuwa ne adaidai lokacin da mahukuntan na birnin Beijing ke neman kara karfin iko da suke da shi a kudancin tekun Indiya inda kasar ke gina wani tsibiri a cikin teku da za ta jibge dakarunta da kayan yaki, abin da kuma ke kara jawo tsamin dangantaka da mahukuntan kasar Japan.