1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta gaza biyan IMF bashi

Yusuf BalaJuly 1, 2015

Asusun bada Lamuni na IMF ya tabbatar da cewa kasar ta Girka ta kasa biyan sama da miliyan dubu na Euro a ranar Talata.

https://p.dw.com/p/1Fr1I
Luxemburg Yanis Varoufakis und Christine Lagarde
Yanis Varoufakis ministan kudin Girka da Christine Lagarde ta IMFHoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

Kasar Girka ta gaza a biyan bashi da kasashen Turai ke binta wanda cikar wa'adin da aka ba ta ya kammala a ranar Talata.

Asusun bada Lamuni na IMF ya tabbatar da cewa kasar ta Girka ta kasa biyan sama da miliyan dubu na Euro, abin zai sa babbar manajar asusun Christine Lagarde ta yi jawabi ga kasashen da suka biyo kasar ta Girka bashi.

Kasuwannin hada-hadar kudade dai sun shiga rudani ganin rashin biyan bashin na Girka zai iya sanya a cire ta daga cikin kasashe da ke amfani da kudin bai daya na Euro, sannan makomar kasar ta ci gaba da kasancewa mamba cikin kungiyar kasashen Turai ya dogara ga kuri'ar raba gardama da za a kada ranar biyar ga wannan wata na Yuli ko al'ummar kasar zasu zabi ci gaba da sanya musu sharuda na tsuke bakin aljihu ko kuma a a.