1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Habasha ta ayyana dokar tabaci

Yusuf Bala Nayaya
February 16, 2018

Kasar Habasha a ranar Juma'a ta ayyana dokar tabaci bayan da Firaminista Hailemariam Desalegn ya bayyana aniya ta sauka daga kujerarsa biyo bayan tashin hankali da rikicin siyasa da kasar ta shiga.

https://p.dw.com/p/2spal
Äthiopien Regierung Soldaten ARCHIV
Habasha ta shiga rudani ta fiskoki da dama da suka hadar da siyasa da zamantakewaHoto: picture alliance/AP Photo/ltomlinson

Majalisar ministocin kasar ce dai ta Habasha ta kai ga cimma wannan matsaya ta sanya dokar tabacin a cewar hukumar yada labaran kasar ta EBC.

Kawancen EPRDF masu mulki sun gana a wannan rana ta Juma'a a cewar EBC sai dai jawaban ministocin bai fayyace tsawon wane lokaci ne dokar tabacin za ta yi aiki ba. Sama da firsinonin siyasa 600 ne dai a ka saki a kasar ta Habasha tun daga watan Janairu sai dai har kawo yanzu al'umma sun gaza gamsuwa da tafiyar da harkokin masu mulki a kasar.