1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar India da Gidauniyar Clinton sun shirya horar da jamián lafiya domin jinyar masu cutar kanjamau

February 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7T

Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton tare da gwamnatin kasar India sun baiyana wani shirin hadin gwiwa na horar da jamián lafiya a game da kula da masu cutar kanjamau. Kasar India ita ce ta fi kowace kasa a duniya yawan mutane da suka kamu da cutar kanjamau. Daga cikin alúmar kasar India miliyan dubu daya, fiye da mutane miliyan biyar da dubu dari daya na dauke da kwayar cutar HIV / AIDS. An cimma yarjejeniyar Shirin hadin gwiwar ne tsakanin kungiyar yaki da cutar kanjamau ta kasar India da gidauniyar Clinton. A jawabin sa tsohon shugaban na Amurka Bill Clinton bayan da ya ziyarci cibiyoyin kimmiya na kasar India yace jamia´n Nurse Nurse na da muhimmiyar rawar takawa wajen kulawa da kuma jinyar masu dauke da cutar HIV. Yace jamián Nurse Nurse baya ga kulawa da majinyata,sun kuma kasance masu bada shawarwariga marasa lafiya domin debe mus kewa ta wariya da kyama da akan nunawa masu wannan larura.A watan da ya gabata, Clinton ya sanar da wani shiri tare da kamfanoni tara masu hada magunguna wanda ya ce zai taimaka wajen rage tsadar kudi da majiyaci kann kashe wajen binciken gano kwayar cutar da kuma maganin ta a kasashe 50 masu tasowa.