1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Indonesiya Na Ci Gaba Da Fama Da Yakin Basasa

January 4, 2005

Duk da bala'in ambaliyar ruwan da ya rutsa da lardin Aceh na kasar Indonesiya, amma har yau ana ci gaba da fafatawa tsakanin sojoji da 'yan tawaye masu neman ballewar lardin daga kasar Indonesiya

https://p.dw.com/p/Bvdp
Kayan taimako sun fara isa Aceh a Indonesiya
Kayan taimako sun fara isa Aceh a IndonesiyaHoto: AP

Watanni kadan bayan nadinsa kan karagar mulki, sabon shugaban kasar Indonesiya Susilo Bambang na fuskantar wani jan aiki a gabansa. Domin kuwa kasar Indonesiya ita ce ta fi kowace kasa zautuwa daga bala’in ambaliyar tekun da ya rutsa da kasashen Asiya makon da ya wuce. Wani abin da ya kara dagula lamarin ma shi ne kasancewar bala’in ya rutsa ne da wani yankin kasar da aka yi shekara da shekaru ana fama da yakin basasa a cikinsa. A ‚yan makonnin da suka wuce, kafin afkuwar bala’in ambaliyar tekun, aka tasa keyar gwamnan yankin zuwa kurkuku bisa zarginsa da laifin cin hanci, lamarin dake yi nuni da mawuyacin halin da ake ciki a lardin daidai da sauran lardunan kasar Indonesiya. Matsaloli na siyasa na hana ruwa gudu ga ayyukan kungiyoyin taimako na kasa da kasa. A da yawa daga cikin kasashen da ambaliyar tekun ta tsunami ta rutsa da su akwai kungiyoyi na cikin gida dake aiki kafada-da-kafada da kungiyoyin taimako na kasa da kasa. Amma a lardin Ache lamarin ya banbanta. A wannan lardi sojojin Indonesiya ne kadai ke da ikon tafiyar da matakan taimakon. Tun dai abin da ya kama daga shekarar 1976 ake fama da zub da jini a yakin basasar da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun ‚yan tawayen dake neman ballewar lardin Aceh daga kasar Indonesiya. Wannan yaki yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu 12. Tun bayan da Susilo Bambang Yudhoyono ya dare kan karagar mulki yake nanata maganar neman bakin zaren warware rikicin Aceh da na sauran yankunan Indonesiya a cikin ruwan sanyi. Amma fa duk da kiran tsagaita wuta da shugaban yayi, sakamakon ambaliyar tsunami, ana ci gaba da gwabza fadan ba kakkautawa. Bayan shekaru 30 na mulkin kama-karya, har yau sojoji na da fada a ji a siyasar Indonesiya. Domin shawo kan wannan lamari shugaba Yudhoyono ya dakatar da aikin dokar ko-ta-kwana ta soja dake ci a lardin Aceh aka kuma ba wa kungiyoyin taimako na kasa da kasa cikakkiyar damar kutsawa yankin. Mai yiwuwa wannan mataki da ya dauka ya karya alkadarin sojoji da ‚yan tawayen da ba sa ga maciji da juna. Ita kanta girgizar kasar da ta haddasa ambaliyar tekun a cikin kiftawa da Bisimillah ta wayar da kan ‚yan tawayen cewar tilas ne su yi cude-ni-in-cude-ka da sauran ‚yan uwa domin shawo kan barnar da ambaliyar ta haddasa. Idan har a karshe an kai ga cimma zaman lafiya, su kuma ragowar mazauna yankin suka farga cewar su ma dai wani bangare ne na kasar Indonesiya mai jinsunan kabilu dabam-dabam kuma taimakon da ake bayarwa ya kai ga ma bukata a maimakon aljifan mahukunta, to kuwa ana iya cewar kwalliya ta mayar da kudin sabulu dangane da matakan shugaba Yudhoyono.